Sauya salon zanga-zanga: An sako sojoji zuwa titunan Abuja

Sauya salon zanga-zanga: An sako sojoji zuwa titunan Abuja

- Zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS ta fara sauya salo a sassan Najeriya da ta samu karbuwa

- Rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa ana yawan samun kai hari a kan ma su zanga-zangar adawa da ma su zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS

- Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa atisayen 'murmushin kada' da ta kaddamar bashi da alaka da kowacce zanga-zanga

An fito da dakarun soji zuwa kan titunan Abuja domin shawo kan zanga-zangar ENDSARS da ta fara sauya salo.

Zanga-zangar ENDSARS a Abuja ta fara sauya salo tare da neman rikidewa zuwa rikici sakamakon harin da wasu batagari ke kaiwa ma su zanga-zangar.

Batagari a Abuja na kai hari kan ma su zanga-zangar nuna adawa da rundunar SARS da kuma ma su zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS.

Lamarin, a yawancin lokuta, ya haddasa gumurzu tare da zama sanadiyyar raunata mutane da kuma lalata dukiya.

KARANTA: Duk don a rusa gwamnatin Buhari ne - Sheikh Jingir ya fadi manufar masu zanga-zanga

Wasu rahotanni sun bayyana cewa wani daga cikin ma su zanga-zanga ya rasa ransa a asibitin da aka kai shi sakamakon mummunan rauni da wasu batagari suka yi masa a Abuja.

An ga dakarun soji da safiyar ranar Litinin a sanannen shataletalen AYA, wurin da masu zanga-zanga su ka yi niyyar mamayewa.

Sauya salon zanga-zanga: An sako sojoji zuwa titunan Abuja
Sauya salon zanga-zanga: An sako sojoji zuwa titunan Abuja
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta rawaito cewa an ga dakarun soji sun saka garkuwa a kan titin domin tabbatar da cewa ma su zanga-zangar basu rufe hanya tare da haddasa cunkuso ba.

KARANTA: Yadda na samo mana kwangilar tono kabari a kan N2m - Abdullahi Dogo

A jiya, Lahadi, ne rundunar soji ta sanar da cewa sabon atisayen 'murmushin kada' da ta kaddamar bashi da wata nasaba da zanga-zangar da matasa ke yi a kan rushe rundunar SARS da zaluncin 'yan sanda.

A cikin wata sanarwa da hedikwatar tsaro ta fitar (DHQ), kanal Sagir Musa, kakakin rundunar soji ya ce kuskure ne a bayyana cewa an kaddamar da atisayen ne saboda zanga-zangar ENDSARS da ake yi a sassan kasa.

Kanal Sagir ya bayyana cewa rundunar soji ta nuna kwarewar aiki tun bayan barkewar zanga-zangar kusan sati biyu da su ka wuce.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel