Tunda gwamnati ta amsa kokenku lokaci ya yi da ya kamata a daina wannan zanga-zanga - Lawan ga matasa

Tunda gwamnati ta amsa kokenku lokaci ya yi da ya kamata a daina wannan zanga-zanga - Lawan ga matasa

- Shugabannin majalisar dokokin tarayya sun bukaci a kawo karshen zanga-zangar rushe rundunar SARS

- Lawan Ahmed ya ce tunda dai gwamnati ta amsa bukatun masu zanga-zangar kamata yayi yanzu su koma gida

- Ya ce lamarin na matukar takura wa jama'a da ke kasuwancinsu

Shugaban majalisar dattijai na kasar, Ahmed Lawan, ya yi kira ga masu zanga-zangar neman kawo karshen rundunar SARS a fadin Najeriya da su yi hakuri su dakatar da zanga-zangar.

Lawan ya bayyana hakan ne bayan ganawar da ya gudana tsakaninsa da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kuma kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Sun yi ganawar ne a yau Lahadi, 18 ga watan Oktoba, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Lawan ya jadadda cewa ya kamata masu zanga-zangar su janye tunda sun gabatar da kokunsu kuma gwamnati ta dauki mamaki kan haka.

Ya kara da cewa wannan zanga-zanga da ake yi yana takura wa al’umma musamman masu gudanar da harkokin kasuwancinsu.

Tunda gwamnati ta amsa kokenku lokaci ya yi da ya kamata a daina wannan zanga-zanga - Lawan ga matasa
Tunda gwamnati ta amsa kokenku lokaci ya yi da ya kamata a daina wannan zanga-zanga - Lawan ga matasa Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: Facebook

Ya kuma ce hakan na kawo cikas ga tattalin arzikin kasar.

KU KARANTA KUMA: Tsaron Arewa: Ali Nuhu ya sha caccaka a wajen 'yan Najeriya saboda rashin shiga zanga-zanga

“Tun da gwamnati ta amince da bukatun da masu zanga-zangar suka gabatar mata, lokaci ya yi da masu zanga-zangar za su daina, gwamnati na bukatar lokaci domin aiwatar da bukatun masu zanga-zangar,” in ji Lawan.

A nashi bangaren, kakakin majalisar wakilai, Gbajabiamila ya yi kira ga kawo karshen zanga-zangar, inda ya bayyana cewa ba za a iya aiwatar da manufa a dare daya ba.

Ya kuma jinjinawa masu sanya-zangar a kan namijin kokarin da suka yi, ya basu tabbacin cewa suna iya ci gaba da zanga-zangar idan ba a cika masu bukatunsu ba a makonni biyu.

A baya mun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugabannin majalisar dokokin tarayya na cikin wata ganawar sirri a yanzu haka.

Hadimin Shugaban kasa Buhari na musamman a shafukan zumuntar zamani, Bashir Ahmad ne ya tabbatar da hakan a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, @BashirAhmaad a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon wani mai bayar da hannu a titi da masu zanga-zanga suka karrama saboda kwazonsa

A cewar Ahmad, Shugaban kasar na ganawa da Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila kan zanga-zangar da ke gudana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel