Lawan ya dauki nauyin aurar da marayu da marasa gata su 100 a Yobe

Lawan ya dauki nauyin aurar da marayu da marasa gata su 100 a Yobe

- Sanata Ahmed Lawan ya aurar da marayu da marasa galihu su 100 a kananan hukumomi biyu da ke jihar Yobe

- Lawan ya aiwatar da wannan shiri ne domin tallafa wa matasa da suka isa aure amma basu da karfin yi

- Wannan shine karo na biyu da shugaban majalisar dattawan ke aurar da matasa a jihar tasa

Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, a ranar Asabar, ya dauki nauyin auren marayu da marasa gata su 100 a kananan hukumomin Karasuwa da Nguru da ke jihar Yobe.

“Mun kasance a nan domin daukar nauyin auren matasa 50 a Nguru da wasu 50 daga karamar hukumar Karasuwa,” in ji Lawan.

Lawan wanda ya samu wakilcin Ahmed Mirwa, kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, ya ce anyi shirin ne domin tallafawa matasa wadanda suka isa aure amma basu da karfin yi.

Ya ce an yi wa dukkanin amaren kayan daki kama daga kujeru, gado da kuma kayan kicin.

KU KARANTA KUMA: Yunƙurin juyin mulki aka yi wa gwamnan Osun - Kwamishina

Lawan ya dauki nauyin aurar da marayu da marasa gata su 100 a Yobe
Lawan ya dauki nauyin aurar da marayu da marasa gata su 100 a Yobe Hoto: @DrAhmadLawan
Asali: Twitter

Ya kara da cewa za a horar da ma’auratan sannan a basu tallafi a fanni daban-daban, daidai da jinsinsu domin daukar dawainiyar auren.

Basher Shariff, jagoran shirin a karamar hukumar ya ce an yi wa ma’auratan gwajin lafiya kafin daura masu aure.

Ya kuma ce an zabi wadanda aka aurar ne ta hannun masu unguwa, hakiman kauye da shugabannin matasa.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa kwanan nan Lawan zai sake daukar nauyin auren marasa karfi su 100 a mazabarsa.

KU KARANTA KUMA: A kan tattaro min takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da na tafi ziyarar aiki - Pantami

Wannan sune rukuni na biyu da Shugaban majalisar dattawan ke aurarwa.

A watan Satumba, ya aurar da mutane 100 a kananan hukumomin Bade da Jakusko da ke jihar.

A wani labari na daban, mun ji cewa zanga-zangar neman a kawo karshen rundunar SARS ya dauki sabon salo a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba, lokacin da wani matashi mai suna Demola ya nemi auran budurwarsa a wajen taron.

Idan za ku tuna dai ana gudanar da zanga-zanga a fadin kasar kan neman a soke rundunar SARS sakamakon zarginsu da ake yi da cin zarafin al’umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng