An aika takardar korafi a kan Buhari zuwa UK da USA saboda nadin wani mukami
- Har yanzu batun aika sunan hadimar Buhari, Lauretta Onochie, a matsayin kwamishina a hukumar zabe ya na cigaba da jawo cece-kuce
- Jam'iyyar PDP da dumbin sauran 'yan Najeriya sun nuna adawa da yunkurin Buhari na son bawa Lauretta wannan muhimmin mukami
- Yanzu haka har wata kungiya mai rajin kare mutuncin Najeriya ta aika takardar korafi a kan Buhari zuwa Ingila da Amurka
Wata kungiya mai rajin kare mutuncin Najeriya (Concerned Nigerians) ta yi Allah wadai da yunkurin shugaba Buhari na son nada Lauretta Onochie a matsayin kwamishiniya a hukumar zabe ta kasa (INEC).
Kungiyar ta roki Amurka, Ingila, da sauran ma su fada a ji a duniya a kan su kawowa Najeriya agaji saboda Buhari ya na shirin lalata siyasar kasa da kassara hukumar INEC.
A takardar da kungiyar ta rubuta ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, ta sanar da USA da UK cewa nadin Lauretta ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
DUBA WANNAN: Muhimman aiyuka 8 na sabuwar rundunar SWAT - NPF
"Kowa ya san 'yar siyasa ce da ke dauke da katin shaidar zama mamba a jam'iyyar APC mai mulki.

Asali: UGC
"Ba iya wannan ne kadai matsalar ba, ta yi kaurin suna wajen ragargaza da cin mutuncin duk wanda ya soki jam'iyyar APC.
"Nada Lauretta, hadimar shugaban kasa, a matsayin kwamishiniya a INEC mai wakiltar jihar Delta ya sabawa kundin tsarin mulki kuma yunkuri ne na lalata kima da martabar hukumar zabe," a cewar takardar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Deji Adeyanju.
KARANTA WANNAN: Neymar ya aika wa Cristiano Ronaldo wasika bayan kamuwa da cutar COVID-19
Har yanzu yumkurin shugaba Buhari na son nada Lauretta na cigaba da yamutsa hazo a cikin kasa.
Babbar jam'iyyar adawa, PDP, da sauran dumbin 'yan Najeriya sun nuna rashin amincewa da niyyar shugaba Buhari ta nada Lauretta a mukami mai muhimmanci kamar kwamishiniya a hukumar INEC.
A wani labarin, hukumar da ke kula da matasa masu yiwa kasa hidima NYSC a jihar Anambra ta hada liyafar taya matasa 12 murnar yin aure a yayin bautar kasarsu ta shekara daya a jihar.
Ma'auratan da suka hadu a rukunin C na masu yiwa kasa hidimar na shekarar 2019, sun hada da Henry Nwachoko, Charles Ruth, Oluchukwu Davis, da Ohale Nkemakolam.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng