Majalisa ta bankado N122bn da NHIS ta jibge a banki a sirrance

Majalisa ta bankado N122bn da NHIS ta jibge a banki a sirrance

- Majalisar dattijai ta bankado wasu makudan kudade da hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS) ta jibge a wani asusun banki

- Wannan ba shine karo na farko da sunan hukumar NHIS ya shiga bakin duniya ba saboda zargin badakala

Majalisar ta mayar da hankali a kan hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS) bayan ta gano N122bn da hukumar ta jibge a wani banki ba tare da sanin gwamnatin tarayya ba.

A cewar majalisar dattijai, hukumar NHIS ta jibge makudan kudaden ba tare da sani ko samun izini daga ofishin babban mai bin diddigin kudin gwamnatin tarayya ba.

Da ya ke kwarmata zancen ranar Juma'a yayin zaman majalisar dattijai, Sanata Matthew Urhoghide, ya ce an samu ribar N3.7bn daga ajiyar kudaden a banki.

KU KARANTA: Gwamantin Buhari ta bayyana sabbin hanyoyin da za ta samu kudaden shiga

Tun a shekarar 2015 kwamitin majalisa ya karbi takardar korafi daga ofishin AGF a kan NHIS bayan bin diddigin kudin da hukumar ta karba daga FG.

Majalisa ta bankado N122bn da NHIS ta jibge a banki a sirrance
Majalisar dattijai
Asali: Facebook

Da ya ke kare NHIS, babban sakataren hukumar, Farfesa Nasir Sambo, ya ce doka ta bawa NHIS damar yin amfani da kudadenta domin a juyasu a sami riba.

Kazalika, ya bayyana cewa ba FG ce ke bawa hukumar NHIS kudade ba.

DUBA WANNAN: Ethiopia ta yi murnar shiga sabuwar shekara 2013 a yayin da kasashen duniya ke hangen 2021

Sai dai, Sanata Urhoghide ya katse hanzarin Farfesa Sambo ta hanyar sanar da shi cewa ribar da aka samu daga kudaden kamata ya yi su shiga aljihun FG.

Sanata Urhoghide, mamba a jam'iyyar PDP daga jihar Edo, ya bukaci NHIS ta zo da takardun shaidar hada-hadar kudi na asusun da aka gano kudaden yayin zaman majalisa na ranar Talata mai zuwa.

A wani labarin, Ministar kudi, kasafi da tsare tsaren kasa, Dr. Zainab Ahmed, a ranar Laraba, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da gano hanyoyin samawa kasar kudaden shiga.

Da ta ke jawabi a taron tattalin arzikin Nigeria karo na 26, Ahmed ta bayyana cewa, babbar matsalar da ke addabar gwamnati a yau shine rashin kudaden shiga don gudanar da manyan ayyuka.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel