Kudu maso Gabas ta na raɓar Arewa ta-tsakiya wajen neman mulki

Kudu maso Gabas ta na raɓar Arewa ta-tsakiya wajen neman mulki

- Mutanen Ibo sun zo yankin Arewa domin su fara yakin neman zaben 2023

- Afam Ezenwafor ya bayyana cewa sun soma neman goyon baya tun yanzu

- Ezenwafor ya na ganin idan su ka hada-kai da sauran bangarori, to za a dace

Wasu daga cikin mutanen yankin Kudu maso gabashin Najeriya, sun fara zama da takwarorinsu na tsakiyar Arewacin kasar nan a kan 2023.

Daily Trust ta ce an yi wani zama a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba, 2020, tsakanin mutanen Ibo da ‘yan Arewa a Makurdi, jihar Benuuwai.

‘Yan siyasar da su ke bayan wanan sabon kawance sun bayyana shirinsu a lokacin da su ka zanta da manema labarai ta bakin wani jagoran tafiyar.

KU KARANTA: Jakadar Birtaniya a Najeriya ta zo Legas, ta yi zama da Tinubu

Shugaban ‘yan APC a majalisar dokokin jihohin Kudu maso gabashin kasar nan, Cif Afam Ezenwafor, yana cikin manyan wannan kungiyar.

Afam Ezenwafor ya bayyana cewa sun zo Arewa ta tsakiya ne domin nema wa yankinsu goyon-bayan sauran bangarorin kasar a zabe mai zuwa.

“Ba za mu iya yi babu Arewa ta tsakiya ba, kuma wannan yanki ya na tsakiyar kasar nan. Abin da ke rike Najeriya shi ne yankin tsakiyar Arewa.”

Ezenwafor ya ce samun hadin-kan wannan yanki ne zai sa Kudu maso gabas ta ci zabe a 2023.

KU KARANTA: Wasu na so Uzor Kalu ya gaji Buhari a 2023

Kudu maso Gabas ta na raɓar Arewa ta-tsakiya wajen neman mulki
Gwamnonin Kudu a taro Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Mista Ezenwafor ya fara neman goyon bayan ‘yan siyasar wannan bangare da ya ke ganin sun yi wa Najeriya waigi domin su kai ga ci a zaben 2023.

Shugaban wannan tafiya, George Ugwuja, ya ce kungiyarsu ta na dauke da duka ‘yan siyasar da su ke nemi takarar majalisar dokoki a yankin Ibo a 2019.

Kwanan na ne kuma ku ka ji wata kungiya ta magoya bayan Bola Tinubu, ta kaddamar da yakin neman takarar shugaban kasar tsohon gwamnan na Legas.

A daidai wannan lokaci kuma ana ganin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai yi takarar kujeran shugaban kasa a karkashin PDP a 2023.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel