Kasafin kudi: Za a karkare zama a kan kundin 2021 a farkon Disamba

Kasafin kudi: Za a karkare zama a kan kundin 2021 a farkon Disamba

- Sanatoci za su kammala zama a kan kasafin kudin shekarar badi a Disamba

- Sanata Barau Jibrin ya bayyana wannan a lokacin da ya zauna da ‘yan jarida

- Majalisa za ta bada dama ga mutane su tattauna a kan kasafin kudin na 2021

Majalisar dattawa ta sha alwashin amince wa da kundin kasafin kudin Najeriya na Naira tiriliyan 13.08 a cikin farkon watan Disamba mai zuwa.

Barau Jibrin, shugaban kwamitin kasafi a majalisar dattawa, ya ce za su gama aikin kundin kasafin, su amince da shi a ranar 3 ga watan Disamba.

Jibrin ya ce za su yi zaman sauraron jama’a a tsakanin 9 da 10 ga watan Nuwamba, 2002, domin a ba ‘yan Najeriya damar sa-baki a kan kasafin na su.

KU KARANTA: Atiku ya ci gyaran kasafin kudin 2021

Kwamitoci da za su zauna za su gabatar da rahotonsu a zauren majalisa ne tsakanin ranar 11 zuwa 18 ga watan Nuwamban inji Sanata Barau Jibrin.

Jaridar Daily Trust ta ce Sanatocin sun fara kokawa da karancin kudin shigan da hukumomi da ma’aikatun gwamnati su ke tatsowa a Najeriya.

‘Yan majalisar dattawan sun nuna cewa dole gwamnati ta dage sosai wajen neman kudin shiga.

Sanatocin sun yi kira game da gina abubuwan more rayuwa da kuma rage kashe facakar kudin kasa, wanda su ke cin kaso mai tsoka a kasafin.

KU KARANTA: FEC: Dangote zai yi wani titi a Legas a maimakon ya biya haraji

Kasafin kudi: Za a karkare zama a kan kundin 2021 a farkon Disamba
Buhari a Majalisa Hoto: Twitter/BashirAhmaad
Asali: Twitter

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya zargi hukumomi da ma’aikatun gwamnati da rashin maida duka kudin da su ka tatso zuwa asusun kasa.

“Akwai hukumomin gwamnati da-dama da ya kamata a ce su na tatso kudi, kuma su na yin hakan, amma ba su kawo duka abin da ya kamata su kawo.”

Idan za ku tuna a makon nan ne wasu Sanatocin jamiyyar hamayya su ka caccaki kundin kasafin kudin 2021 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar.

'Yan majalisa sun bankado inda za a iya samun matsala da kundin kasafin kudin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel