Shugaban 'yan sandan Najeriya ya gargadi jami’an rundunar a kan amfani da karfi kan masu zanga-zanga

Shugaban 'yan sandan Najeriya ya gargadi jami’an rundunar a kan amfani da karfi kan masu zanga-zanga

- Sufeto Janar na yan sanda, Muhammad Adamu, ya ja kunnen jami'an rundunar a kan masu zanga-zanga

- IGP ya bukaci da kada su yi amfani da karfi a kan masu tattakin

- Ya ce a matsayinsu na yan kasa suna da yancin bayyana ra'ayinsu, haduwa da kuma yin gangami

Shugaban yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya gargadi dukkanin jami’an yan sanda a fadin kasar kan amfani da karfi ga masu gudanar da zanga-zangar lumana.

A cewar wata sanarwa daga kakakin rundunar yan sanda; DCCP Frank Mba, Shugaban yan sandan ya bayyana cewa yan kasa na da yancin nuna ra’ayinsu, haduwa, da kuma yin tattaki wanda ya zama lallai a ce yan sanda sun kare su a koda yaushe.

KU KARANTA KUMA: Guntun gatarin ka: Yadda wata mata mai ƴar kucilar mota ta ja hankalin jama'a a yanar gizo

Shugaban rundunar a ranar Alhamis, 15 ga watan Oktoba, ya roki masu zanga-zangar da su ci gaba da gudanar da zanga-zangarsu cikin lumana, gidan talbijin din Channels ta ruwaito.

Shugaban 'yan sandan Najeriya ya yi gargadi jami’an rundunar a kan amfani da karfi kan masu zanga-zanga
Shugaban 'yan sandan Najeriya ya yi gargadi jami’an rundunar a kan amfani da karfi kan masu zanga-zanga Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Ya kara da cewar rundunar ta ji koken da jama’a suke yi sannan cewa za ta yi iya bakin kokarinta wajen gano bakin zaren matsalolin da kuma hukunta duk yan sandan da aka samu da hannu wajen aikata laifin.

Har ila yau ya yi alkawarin kara inganta kyakyawar alaka ta zamantakewa a tsakanin 'yan sanda da jama’ar gari.

KU KARANTA KUMA: Ya isheku haka: Masoya Buhari sun gargadi ma su zanga-zanga

A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya ta koka cewa daliban jami'o'in Najeriya da ya kamata ace sun koma makaranta ne aka dauka suna zanga-zangan #EndSARS a fadin tarayya.

Ta daura laifin kan yajin aikin da kungiyar Malaman jami'a ASUU suke yi.

Ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige, ya bayyana hakan ne a zaman sulhun da ya jagoranta tsakanin gwamnati da jami'an ASUU ranar Alhamis a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel