Kasar Ethiopia ta yi murnar shiga sabuwar shekara 2013 a yayin da kasashen duniya ke hangen 2021

Kasar Ethiopia ta yi murnar shiga sabuwar shekara 2013 a yayin da kasashen duniya ke hangen 2021

- A yayin da sauran kasashen duniya ke hango sabuwar shekarar 2021, kasar Ethiopia ta shiga shekarar 2013

- Akwai tazarar shekaru 7 a tsakanin kasar Ethiopia da sauran kasashen duniya saboda kasar ta na amfani da wata kalenda ta daban

- Kasar Ethiopia ta na amfani da kalendar 'Coptic' a yayin da sauran kasashen duniya ke amfani da kalendar 'Gregorian'

A cikin watan Satumba da ya gabata ne kasar Ethiopia ta yi murnar shiga sabuwar shekarar 2013 duk da sauran kasashen duniya su na cikin watannin karshe na shekarar 2021.

Duk da ana taka tsan-tsan a duniya saboda bullar annobar korona, hakan bai hana kasar Ethiopia gudanar da bukukuwan shigowar sabuwar shekarar 2013 ba.

Hakan na nufin kenan sauran kasashen duniya sun sha gaban kasar Ethiopia da shekara 7.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya bayyana dalili

Dalilin faruwar hakan kuwa shine saboda kasar Ethiopia ta na amfani da wata tsohuwar kalenda da tun karni na 16th aka daina amfani da ita a Turai.

Kalendar da su ke amfani da ita sunanta 'Coptic' kuma tana da tsari daidai da na kalendar 'Julian'.

Kasar Ethiopia ta yi murnar shiga sabuwar shekara 2013 a yayin da kasashen duniya ke hangen 2021
Kasar Ethiopia ta yi murnar shiga sabuwar shekara 2013 a yayin da kasashen duniya ke hangen 2021
Asali: UGC

A yayin da kasar Ethiopia ke amfani da kalendar 'Coptic', sauran kasashen duniya suna amfani da kalendar 'Gregorian', mai dauke da kwanaki 365 a shekara.

DUBA WANNAN: Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure

A cewar wani shafin yanar gizo, Face2FaceAfrica, an samu wannan banbanci ne tun lokacin da Cocinan kasar Ethiopia suka ki amincewa da Roman Katolika a kan lokacin haihuwan Yesu Almasihu.

Ita kalendar 'Gregorian' an tsarata ne bisa lissafin shekarar haihuwar Jesus, yayin da ita kuma kalendar 'Coptic' an tsarata ne bisa lissafin daukar cikin Jesus, ba haihuwarsa ba, kamar yadda masanin tarihi mai suna Annianus, dan kasar Masar ya rawaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel