Kungiya ta rubutawa Shugabannin Intel takarda bayan an kori Ma’aikata 600

Kungiya ta rubutawa Shugabannin Intel takarda bayan an kori Ma’aikata 600

- Kungiyar Ma’aikata ta rubutawa Intel takarda bayan ta kori mutane aiki

- An ba Intel mako daya su dawo da wadanda su ka kora ko kuma ayi bore

- MWUN ta ce za ta janye aiki daga kamfanin idan ba a yi abin da ta ce ba

Kungiyar ma’aikatan ruwa na Najeriya, MWUN, ta tsoma bakinta a lamarin kamfanin Intel da daruruwan ma’aikatan da su ka kora daga aiki.

A ‘yan kwanakin nan ne kamfanin Intel ya sallami ma’aikata 600. Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ne su ke da wannan kamfani.

MWUN ta rubuta wasika zuwa ga shugaban sashen kula da ma’aikata na kamfanin Intel da ke Fatakwal, ta na neman dawo da wadanda aka sallama.

KU KARANTA: Manyan 'yan siyasa sun hadu a auren 'Ya 'yan Atiku da Ribadu

Kungiyar MWUN ta bukaci Mista M. Ndon ya duba wannan kora da ya sa wa hannu ko kuma su dakatar da aikin kamfanin a duka ofisoshin a Najeriya.

Wannan wasika ta shiga hannun ‘yan jarida ne a ranar Laraba, 14 ga watan Oktoba, 2020.

Takardar da ta fito daga ofishin sakataren MWUN, Felix Akingboye, ta yi wa Intels Nigeria barazana, ta ce ba a biya wadanda aka kora hakkokinsu ba.

Felix Akingboye ya ce:

KU KARANTA: Ministar kudi ta bayyana yadda Gwamnati za ta raba ayyuka a 2021

Kungiya ta rubutawa Shugabannin Intel takarda bayan an kori Ma’aikata 600
Ofishin Intel Nigeria Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Abin takaici, mun samu labarin cewa kun dakatar da mutane daga aiki, wanda hakan ya jawo mutane 300 (‘yan kungiyarmu) su ka rasa abin yi.”

Kungiyar ta ce an yi wannan ne ba tare da an biya ma’aikatan kudin sallamarsu ba.

“Mu na bukatar abubuwa su cigaba da tafiya yadda su ke, har sai an ci ma matsaya game da kudin sallamarsu. MWUN ta bada mako guda domin ayi wannan.

Kwanan nan ne ku ka ji cewa Atiku Abubakar ya dawo Najeriya bayan kwashe watanni tara a Dubai, ya dawo ne domin ya yi wa wasu jama'a ta'aziyya.

Atiku Abubakar ya sauka gida ne ta filin jirgin Nnamdi Arzikwe da ke birnin tarayya Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel