Tarar N10bn: Na shirya yafewa Adams Oshiomole - Gwamna Samuel Ortom

Tarar N10bn: Na shirya yafewa Adams Oshiomole - Gwamna Samuel Ortom

- Gwamna Samuel Ortom da tsohon gwamnan Edo sun gurfana gaban kuliya

- Ortom ya ci tarar Oshiomole bilyan 10 kan zargin sharrin da yayi masa a 2018

- Yayinda Oshiomole ke bada hakuri, Ortom yace shirya yake ya yafe amma da sharruda

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Laraba ya tabbatarwa tsohon shugaban uwar jam'iyyar All Progressives Congress APC, Adams Oshiomhole, cewa shirya yake ya yafe masa idan ya nemi afuwa.

Ortom ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai yayinda yake rabawa shugabannin kananan hukumomi motoci 23 da shugabannin majalisar dokokin jihar a Makurdi, Punch ta ruwaito.

DUBA NAN: An damƙe wanda ya maye gurbin Gana

Mun kawo muku cewa tsohon shugaban kasan jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya bukaci ayi ta ta kare tsakaninsa da gwamna Samuel Ortom ba tare da an kai ga kotu ba.

Kwanaki gwamnan jihar Benuwai Samuel Ortom ya maka Adams Oshiomole a kotu, ya bukaci ya biya sa Naira biliyan 10 bisa zargin yi masa karya.

Tarar N10bn: Na shirya yafewa Adams Oshiomole - Gwamna Samuel Ortom
Adams Oshiomole - Gwamna Samuel Ortom Credits: @sourcenigeria
Asali: Twitter

Idan za ku tuna a watan Yulin 2018 ne Adams Oshiomole ya kira taron manema labarai, inda ya zargi Samuel Ortom da hannu a kisan wasu fastoci biyu.

Mai kare tsohon shugaban jam’iyyar APC ya fadawa Alkali Augustine Ityonyiman na babban kotu da ke garin Makurdi za su ranar da za su nemi ayi sulhu.

Mai shari’a, Augustine Ityonyiman ya daga shari’ar zuwa 29 ga watan Oktoba domin bangarorin su sasanta.

KU KARANTA: Sabbin mutane 179 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 60,834

Martani kan lamarin, Ortom yace, "Ni Kirista ne kuma Ingila ta ce a yafe masa kura-kuranku kuma zamu yafewa wadanda suka zaluncemu."

"Saboda haka idan dan'uwanka yayi maka laifi kuma ya dawo ya nemi gafara, za ka yafe masa. Bugu da kari akwai sharrudan da aka gindaya, kuma na san ina da gaskiya lokacin da yayi wadannan zarge-zargen."

"Idan ya dawo ya bani hakuri kuma ya koma gidan jaridar da yayi amfani wajen bata min suna ya wallafa neman uzurinsa kuma ya cika sharrudan da lauyoyi na suka gindaya, lallai zan yafe masa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel