Sharaf-sharaf da hawaye: Bidiyon yadda matashi ya ci kuka bayan an ragargaje motarsa a wurin zanga-zanga

Sharaf-sharaf da hawaye: Bidiyon yadda matashi ya ci kuka bayan an ragargaje motarsa a wurin zanga-zanga

- Wasu 'yan batagari dauke da muggan makamai sun kai wa masu zanga-zangar lumana hari a Abuja

- Batagarin, wadanda ake zargin 'yan daba ne, sun ji wa masu zanga-zanga da dama raunuka tare da lalata motoci akalla 5 dake wurin

- Wani matashi da aka ragargaje ma sa mota ya ci kuka sharaf-sharaf da hawaye saboda bakin ciki

Wasu batagari, da ake kyautata zaton 'yan daba ne, dauke da makamai sun kai hari a kan wasu matasa da ke zanga-zanga a kan zaluncin da 'yan sandan rundunar SARS ke yi a fadin Najeriya.

'Yan daban, wadanda ke dauke da adduna, sun kai wa masu zanga-zangar farmaki a daidai Berger, bayan kusan sa'a daya da fara zanga-zangar.

Batagarin matasan sun ci mutuncin masu zanga-zangar har da masu wucewa, inda suka lalata ababen hawa da dama da ke wurin.

Sharaf-sharaf da hawaye: Bidiyon yadda matashi ya ci kuka bayan an ragargaje motarsa a wurin zanga-zanga
Wurin da 'yan daba suka kai hari kan ma su zanga-zanga a Abuja
Asali: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan dabar sun lalata akalla motoci 5 nan take, sannan sun ji wa masu zanga-zanga da dama munanan raunuka.

DUBA WANNAN: Muhimman aiyuka 8 na sabuwar rundunar SWAT - Rundunar 'yan sanda

Wani matashi daga cikin wadanda aka ragargajewa mota ya ci kuka sharaf-sharaf da hawaye saboda bakin ciki.

A wani labarin mai nasaba da wannan, Legit.ng Hausa ta wallafa cewa babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya samar da sashen jami'an da suka kware a sarrafa makamai da fada (SWAT) domin maye gurbin sashen jami'an SARS da aka rushe.

KARANTA: Babbar magana: Buhari zai ruguje EFCC da ICPC, ya bayyana dalili

Mambobin wannan sabon sashen za su samu horo da kuma jarabawar kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya gudanar da wannan muhimmin aiki.

Za su fara samun horo a sansanonin horar da jami'an rundunar 'yan sanda daban daban da ke fadin kasar, a mako mai zuwa.

Za a horas da jami'an rundunar da ke a shiyyoyin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu a sansanin horas da jami'an na Nonwa-Tai, jihar Rivers.

Kazalika, rundunar 'yan sanda ta fitar da jerin muhimman aiyukan sabuwar rundunar SWAT.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel