Muhimman aiyuka 8 na sabuwar rundunar SWAT - NPF

Muhimman aiyuka 8 na sabuwar rundunar SWAT - NPF

- A ranar Talata ne aka sanar da samar da sabon sashe a rundunar, na kwararrun jami'ai a sarrafa makamai da yaki (SWAT) kuma za a fara yi masu horo mako mai zuwa

- Matasa ma su zanga-zanga sun nuna rashin amincewa da kafa sashen SWAT domin maye gurbin SARS

- Rundunar 'yan sanda, bayan sauraron korafin matsan, ta zayyana aiyukan sabuwar rundunar SWAT

Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya samar da sashen jami'an da suka kware a sarrafa makamai da fada (SWAT) domin maye gurbin sashen jami'an SARS da aka rushe.

Mambobin wannan sabon sashen za su samu horo da kuma jarabawar kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya gudanar da wannan muhimmin aiki.

Za su fara samun horo a sansanonin horar da jami'an rundunar 'yan sanda daban daban da ke fadin kasar, a mako mai zuwa.

Za a horas da jami'an rundunar da ke a shiyyoyin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu a sansanin horas da jami'an na Nonwa-Tai, jihar Rivers.

KARANTA: Kotu ta yankewa barawon molin buga bulo hukuncin daurin shekara guda

Haka zalika, za a horas da jami'an rundunar 'yan sandan shiyyar Arewa da Kudu maso Yamma a kwalejin horas da 'yan sandan sintiri da ke Ende, jihar Nasarawa da kuma wacce ke Ila-Orangun, jihar Osun.

Muhimman aiyuka 8 na sabuwar rundunar SWAT - NPF
Frank Mba
Asali: UGC

Muhimman abubuwa dangane da sabon sashen runduna ta (SWAT).

Wannan sabon sashi na musamman yana da iko ne kaɗai akan:

1. Maida martani kan hare-haren da suka shafi fashi da makami.

2. Maida martani a wuraren da ake aikata laifuka da muggan mukamai.

3. Ayyukan ceton rai.

4. Atisaye na musamman wanda ya ƙunshi fitattun masu aikata manyan laifuka.

KARANTA: Zanga zangar #EndSARS: Aisha Yesufu ta aike da muhimmin sako ga matasan Nigeria

5. Babu wani jami'i daga rusasshiyar rundanar yaƙi da fashi da makami (SARS) da zai kasance a sabuwar runduna ta musamman(SWAT).

6. Atisayen sabon sashe na musamman na rundunar SWAT zai zamana na hankali.

7. Sabbin jami'an sabon sashen ba zasu ke fita samamen yau da kullum ba.

8. An haramtawa jami'an sashen bincike ko caje wayoyi, na'ura mai ƙwakwalwa da sauran na'urorin zamani ba bisa ƙa'ida ba.

9. Jami'an sabuwar rundunar ta musamman dole su kasance tsarkakakku daga dukkan laifuka, za su kasance ma su ɗa'a kuma ba zasu yi amfani da bindigogi ba bisa ƙa'ida ba ko cin zarafin haƙkoƙin bil'adama.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun DCP FRANK MBA, Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel