An gudanar da zanga-zangar goyon bayan gyara SARS a Kano (hotuna)

An gudanar da zanga-zangar goyon bayan gyara SARS a Kano (hotuna)

- Kungiyoyin matasa a Kano sun gudanar da zanga-zangar goyon bayan gyara rundunar SARS a jihar

- Matasan sun nuna gamsuwa matuka da mayar da sauya wa rundunar suna zuwa SWAT da IGP ya yi

- Sun ce soke rundunar ba ita ce mafita ba a yanzu

Matasa a jihar Kano sun yi zanga-zangar goyon bayan yin garambawul a rundunar yan sandan SARS amma ba wai a soke ta ba.

Idan zai ku tuna ana gudanar da zanga-zangar neman a soke rundunar SARS a fadin kasar inda yankin kudancin kasar suka fi ba kiran karfi.

A yayinda suke tattakin a Kano, an gano matasa dauke da kwalayen sanarwa inda suke nuna godiya ga Shugaban rundunar yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, a kan sauya wa rundunar suna da ya yi zuwa SWAT.

KU KARANTA KUMA: Ka da ka yi gaba da kowa, yau kaine Sarkin Zazzau: Saƙon Elrufai ga Bamalli

An gudanar da zanga-zangar goyon bayan gyara SARS a Kano (hotuna)
An gudanar da zanga-zangar goyon bayan gyara SARS a Kano Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Sun kasance dauke da rubutu kamar haka: “Gangamin yin garambawul a rundunar SARS. #Godiya ga IGP a kan garambawul da ya yi wa rundunar SARS. ‘Kawo karshen rundunar SARS ba shine mafita ba.”

KU KARANTA KUMA: Abun mamaki: Saurayi ya nemi auren budurwa a taron zanga zangar EndSARS, ta amince

Shugaban haɗakar ƙungiyoyin matasa da ke goyon bayan sabuwar rundunar SWAT da za ta maye gurbin SARS, Khalid Sunusi Kani, ya shaida wa sashin BBC cewa su suna so ne a gyara ayyukan rundunar SARS ba wai a rushe ta ba.

Ga hotunan gangamin:

An gudanar da zanga-zangar goyon bayan gyara SARS a Kano (hotuna)
An gudanar da zanga-zangar goyon bayan gyara SARS a Kano Hoto: @bbchausa

A wani labarin, Babajide Sanwo-Olu, gwamnan jihar Legas ya ce gwamnatin jihar ta ware kudi har naira miliyan 200 domin biyan diyya ga iyalan da jami'an rundunar SARS suka kashe musu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga masu zanga-zangar a gaban majalisar jihar Legas a ranar Talata.

Sanwo-Olu ya ce an ware kudaden ne domin tallafa wa iyalan wadanda 'yan sandan suka kashe bisa kuskure.

Ya ce an samo jerin sunayen wadanda 'yan sandan suka kashe kuma ana sake bincikawa domin tabbatar da cewa ba a cire sunan kowa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel