Zargin karkatar da tallafin Korona: An tsige shugaban kungiyar dalibai ta kasa 'NANS'
- NANS, babbar kungiyar daliban jami'o'in Najeriya, ta dakatar da shugabanta, Mista Danielson Akpan
- An dakatar da Mista Akpan ne bayan samunsa da laifin karkatar da tallafin annobar korona da aka bawa kungiyar
- Kwamitin bincike ya ce Mista Akpan ya hau yi wa mambobinsa barazanar rabasu da ransu don kar su fitar da sakamakon bincike
Kungiyar daliban Najeriya (NANS) ta sanar da tsige shugabanta, Danielson Akpan, bisa zarginsa da almundahanar kudi.
Shugabanni da ma su ruwa da tsaki a NANS sun dade su na gunaguni a kan jagorancin Mista Akpan saboda ya kara watanni 12 a kan zangon mulkinsa da ya fara tun watan Yuli na shekarar 2018.
Sanarwar tsige Mista Akpan ta fito ne bayan wani taro da majalisar kungiyar ta yi ta yanar gizo a ranar Talata.
DUBA WANNAN: Bidiyon yadda ma su zanga-zanga su ka kwaci dan sanda a hannun 'yan daba
Tun da farko, shugaban majalisar kungiyar NANS, Gambo Abu Mohammed, ya kafa kwamitin binciken Mista Akpan bisa zarginsa da karkatar da tallafin annobar korona da aka bawa kungiyar.
A yau, Talata, ne kwamitin ya gabatar da rahoton cewa an samu Mista Akpan da laifin karkatar da tallafin korona da kuma boye wasu muhimman bayanai da za su kawowa kungiyar NANS cigaba.
"Mun same shi da laifin karkatar da kudin da ya karba da sunan kungiya a matsayin tallafin annobar korona.
DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 15 a jihar Borno
"Sannan ya shiga yi wa mambobin kwamitin bincike da shugaban majalisa barazana don kar su fitar da rahoton sakamakon bincikensa," a cewar sanarwar da NANS ta fitar.
Hallayar Mista Akpna, a cewar kwamitin bincike, ya jawowa kungiyar NANS zubewar mutunci da kima a idon jama'a.
A wani labarin, Adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Nigeria ya kai 60,655 a daren ranar Talata biyo bayan sabbin mutane 225 da suka kamu da cutar.
Jihar Lagos na da sabbin mutane 165 daga cikin 225, sai babban birnin tarayya Abuja da ke bin Lagos da mutane 17, yayin da Rivers ke da mutane 13.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng