EndSARS: Gwamnan Lagas ya gana da Buhari a Aso Rock

EndSARS: Gwamnan Lagas ya gana da Buhari a Aso Rock

- Gwamnan jihar Lagas, Sanwo-Olu ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Villa

- Sannwo-Olu ya yi tattaki zuwa villa ne saboda zanga-zangar kawo karshen SARS a jihar Lagas

- Ya kuma gabatar wa da shugaban kasar bukatun masu zanga-zangar

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Lagas ya gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan hauhawan zanga-zangar kawo karshen rundunar SARS a jihar Lagas.

Gwamnan, a wani wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a yau Talata, ya ce: “Na gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin gabatar masa da bukatun masu zanga-zangar kawo karshen SARS a Lagas.

EndSARS : Gwamnan Lagas ya gana da Buhari a Aso Rock
EndSARS : Gwamnan Lagas ya gana da Buhari a Aso Rock Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

“Shugaban kasar ya jadadda jajircewarsa wajen ganin ya gyara fasalin rundunar yan sanda gaba daya.

KU KARANTA KUMA: 2023: An bayyana sunayen yan takara 10 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas

Har ila yau gwamnan ya ce: “Za a cimma manufofin wadannan zanga-zanga da aka yi sannan zan ci gaba da aiki domin kare hakkin al’umman jihar Lagas a kullun.

“A yau dinnan Shugaban kasar ya amince da wani kwamiti da ya kunshi shugabannin kugiyoyin jama’a domin duba ga dukkanin cin zarafi da yan sanda suka yi."

Ziyarar nasa na zuwa ne ‘yan sa'o'i kadan bayan ya halarci taron zanga-zangar a Alausa, jihar Lagas, inda ya yi alkawarin gabatar da bukatunsu ga shugaban kasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta tabbatar da alkalan kotun koli 8 (jerin sunaye)

A lokacin ganawar, Sanwo-Olu ya yi alkawarin gidauniyar miliyan N200 domin biyan diyya ga wadanda lamarin ya yi ajalinsu a jihar.

A gefe guda, Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu a ranar Talata ya umurci gaba daya jami'an da ke a sashen dakile fashi da makami SARS da su je shelkwatar rundunar da ke Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel