Malama da Daliban da aka sace a Kaduna sun dawo gida, sun samu ‘yanci

Malama da Daliban da aka sace a Kaduna sun dawo gida, sun samu ‘yanci

- Kwanaki aka sace wasu mutane ana shirin jarrabawar JSCE a Garin Kaduna

- An shafe tsawon kwanaki ana sauraron dawowar wadannan yaran makaranta

- Sai a karshen makon jiya ne aka yi dace su ka samu ‘yanci, su ka dawo gida

Daily Trust ta fitar da rahoto cewa malamar makarantar nan da aka sace a garin Kaduna tare da wasu dalibai, sun samu ‘yanci daga hannun miyagu.

An tsare wadannan Bayin Allah ne kwanaki a garin Damba-Kasaya, a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.

Jaridar ta ce wadanda aka sace sun koma gidajensu a ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, 2020.

KU KARANTA: Kungiya ta fadawa Shugaba Buhari hanyar shawo kan matsalar tsaro

Rahoton ya bayyana cewa mutanen sun isa gidajensu ne da kimanin karfe 8:00 na dare bayan an biya kudi domin karbar fansarsu daga hannun ‘yan bindiga.

Zuwa yanzu, jaridar ba ta iya tabbatar da adadin kudin da dangin ‘yan makarantar su ka biya ba.

Malamar wannan makaranta ta Prince Academy da ke Chikun, Madam Christian Madugu, ta samu ‘yanci ne tare da ‘dalibanta hudu da aka yi garkuwa da su.

Yaran da aka sace su ne: Happy Waziri, Ezra Bako, Miracle Danjuma da Favour Danjuma. Dukkansu matasa ne ‘yan kasa da shekaru 19 da haihuwa.

KU KARANTA: ‘Yan sa-kai sun kama Budurwa, sun yi mata zigidir a Ribas

Malama da Daliban da aka sace a Kaduna sun dawo gida, sun samu ‘yanci
Wasu da aka ceto a Kaduna Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Wani jagoran matasa da ke kauyen Damba-Kasaya mai suna Akila Luka Barde, ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa an saki wadannan mutane a makon da ya wuce.

“An biya kudi, amma ba zan iya fada maku nawa ba ne.” inji Barde.

Tun kwanaki aka yi awon gaba da wadannan yaran makaranta da malamarsu, a wajen wannan hari ne aka rasa ran wani yaro, Benjamin Auta.

Yanzu nan labari ya ke zuwa mana cewa wasu 'yan sanda akalla biyar sun mutu a mumunan hadarin mota, lamarin ya auku ne a jihar Ondo a ranar Talata.

Kakakin hukumar 'yan sandan jihar Ondo, Mr Tee-Leo Ikoro, ya tabbatar da aukuwan lamarin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng