Ruguza rundunar SARS: Ka buɗe idanuwanka da kyau - Shawarar Marafa ga Buhari
- Sanata Kabiru Marafa ya yi tsokaci a kan soke rundunar yan sandan SARS da aka yi a kasar
- Marafa ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya farka daga bacci don kada ya fada a tarkon abokan hamayya
- Jigon na APC ya ce sharrin da ke tattare da soke rundunar SARS ya fi alkhairinsa yawa
Sanata Kabiru Garba Marafa ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bude idanunsa da kyau, cewa zanga-zangar kawo karshen rundunar SARS da aka gudanar a fadin kasar ya kasance makarkashiya da aka yi kan gwamnatinsa.
Marafa wanda ya kasance dan gaba-gaba a takarar gwamna na APC a jihar Zamfara a zaben 2019, ya ce sharrin ruguza rundunar SARS ya fi alkhairinsa yawa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun jikkata wasu uku a Katsina

Asali: Twitter
“Akwai bukatar shugaban kasa ya bude idanunsa sannan ya yi taka-tsan-tsan sosai. Shugaban kasar na iya fadawa tarkon makiyansa. Matsayana shine cewa wasu mutane sun matsu su ga sun tunkude wannan gwamnati ta kowani hali.
"Da wannan zanga-zanga da aka gudanar don kira ga soke rundunar SARS, ina fargaba muna iya shiga cikin manyan matsaloli, musamman daga inda na fito. Daga karshe, wadannan mutanen za su fito su zargi gwamnati da gaza kare kayukar yan kasa,”in ji shi.
“Zan iya bugun kirji na ce maku zanga-zangar ba game da SARS bane, a kan gwamnatin nan ne. Kila wasu mutane basa farin ciki da wannan gwamnati sannan kila suna son haddasa matsala daga wani wuri.
KU KARANTA KUMA: Takaitaccen tarihin 'yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu
"Wani matsala zai haifar da wani, kafin ka sani ya zama matsalar kasa baki daya. Shin za mu iya rayuwa ba tare da SARS ba? Ba zai yiwu ba,” in ji shi.
A wani labarin, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayyana cewa za a fara horar da wani sabon sashin da zai maye gurbin rundunar 'yan sanda ta musamman da aka rushe.
Adamu ya bayyana hakan a ranar Litinin bayan karbar David Adeleke, fitaccen mawaki, a ofishinsa.
Ya jaddada cewa rushe rundunar ya zama dole kuma sai an kara wani tsari domin maye gurbin wancan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng