Takaitaccen tarihin 'yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu

Takaitaccen tarihin 'yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu

- Matakin rusa rundunar SARS da hukumar 'yan sanda ta dauka ta saka murna a zukatan 'yan Najeriya

- Kafin nan zanga-zanga ta barke a dukkan fadin kasar nan inda matasa suka dinga koka wa a kan cin zarafi da zaluncin jami'an

- Aisha Yesufu ta jagoranci matasan kuma ta tabbata 'yar gwagwarmaya wacce aka ganta da hijabi a gaba-gaba

Matakin rusa runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami da aka yi ya jefa 'yan Najeriya cikin murna da jin dadi matuka.

Kafin daukar wannan matakin, wasu 'yan Najeriya sun dade suna kaiwa da kawowa tare da fafutukar neman rusa rundunar wacce aka dade ana zargi da cin zarafi, azabtarwa da kashe jama'a.

Mace mai kamar maza, Aisha Yesufu tana daga cikin jama'ar da suka debi shekaru suna son ganin an samar da mulkin da ya dace a kasar nan, kuma sunanta ya sake bayyana a 2014 wurin fafutukar ceto 'yan matan Chibok da aka sace.

A wannan lokacin, ta ja gaba a wurin zanga-zangar da ke nuna bijirewa tsarin 'yan sanda.

Babban abinda ke banbantata da sauran 'yan gwagwarmaya shine yadda take zama cikin hijabinta a koda yaushe.

Ga takaitaccen tarihin Aisha Yesufu:

- An haifeta a shekarar 1973 a birnin Kano kuma ta girma a cikin birnin.

- 'Yar asalin jihar Edo ce da ke Kudu maso kudancin Najeriya. Ta samu karatunta na digirin farko a jami'ar Bayero.

- 'Yar gwagwarmayar tana da aure har da 'ya'ya.

- Aisha Yesufu ta ce tana bala'in son mijinta kuma baya zuwa wurin gwagwarmayarta saboda shi baya son hayaniya.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe rayuka 12, mutum 9 sun jigata a Kaduna

Takaitaccen tarihin 'yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu
Takaitaccen tarihin 'yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu. Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Masu zanga-zanga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun harbi 'yan sanda 3

A wani labari na daban, dangane da zaben 2023 dake tunkarowa, Hauwa Atiku Uwais, diyar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar tayi alkawarin mara wa mahaifinta baya, indai har ya sake neman takarar shugaban kasar Najeriya.

Hauwa ta bayyana hakan ne jiya a Abuja, lokacin da ake wata tattaunawa akan yadda za'a kawo gyara da cigaban Najeriya. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel