COCONEPD: Dattawa sun yi Allah-wadai da 'shiru' kan rashin tsaro a Gwamnatin Buhari

COCONEPD: Dattawa sun yi Allah-wadai da 'shiru' kan rashin tsaro a Gwamnatin Buhari

- Kungiyar Coalition of Concern Northern Elders for Peace and Development ta yi magana jiya

- COCONEPD ta bayyana cewa sha’anin tsaro ya na kara tabarbarewa a yankin shugaban kasa

- Shugabannin kungiyar sun bayyana Muhammadu Buhari da mutumin kirkin da ake yaudara

A ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba, ‘yan wata kungiyar hadaka ta manyan Arewacin Najeriya ta nuna damuwa game da gum din shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kungiyar da ke kokarin kawowa cigaba da zaman lafiya a Arewa ta koka da yadda shugaban kasar ya yi tsit, a lokacin da ake kiran ya sake wa hukumomin tsaro zani.

A cewar wannan kungiya COCONEPD, kiran da majalisa su ka yi wa shugaban kasar na daukar mataki, ya isa ya sa gwamnatin tarayya ta yi abin daya dace tun wuri.

KU KARANTA: Buhari ya rage kudin lantarki bayan 'yan kwadago sun yi zama da Gwamnati

Jaridar Punch ta ce COCONEPD ta yi wannan jawabi ne ta bakin shugabanta na kasa, Dr Mohammed Suleiman da kuma sakatariyar kungiyar, Hajiya Mairo Buni.

Kungiyar COCONEPD ta bayyana cewa lamarin tsaro ya na kara cabewa a kasar nan, ta ce hakan ya jefa mata da kananan yara a Arewacin Najeriya cikin wani mugun hali.

Mohammed Suleiman da Mairo Buni su ka ce abin da shugaban kasa zai fara shi ne tsige hafsun tsaro.

Dattawan su na ganin cewa kasafin kudin 2021 da shugaban kasa ya gabatar a majalisa, ba zai share hawayen ‘yan kasa idan har gwamnati ba ta dauki matakin gaggawa ba.

KU KARANTA: Buhari ya kaddamar da ginin Jami'ar Kungiyar Izala

COCONEPD: Dattawa sun yi Allah-wadai da rashin tsaro a Gwamnatin Buhari
Shugaban kasa Buhari Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Jawabin na COCONEPD ya ce: “Babu ‘dan Najeriya da ke barci da minshari a yanzu. Gidajenmu da hanyoyi sun cika da 'yan fashi da makami, masu sata, da ‘Yan Boko Haram.”

A jawabinta, kungiyar ta ce shugaban ya na da niyya mai kyau, amma ana boye masa halin da ake ciki.

A jiya kun ji cewa Shugaban kasa ya yi babbar bakuwa a cikin fadar Aso Villa a lokacin da ake shirin shiga matakin karshe na zaben kungiyar kasuwanci na Duniya.

Buhari ya karbi bakuncin tsohuwar Ministar kudi, Ngozi Okonjo-Iweala, sun yi kus-kus.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel