Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU ta shiga ganawar sirri da shugabannin majalisar dattawa kan IPPIS

Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU ta shiga ganawar sirri da shugabannin majalisar dattawa kan IPPIS

- A yanzu haka kungiyar ASUU ta shiga ganawa da jagororin majalisar dattawa

- Suna tattaunawa ne a kan tsarin biyan albashi na IPPIS

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai ya ce ma’aikatan tarayya da ke a tsarin IPPIS ne kadai za su samu albashi

Kungiyar malaman jami’a (ASUU) na cikin ganawar sirri da majalisar dattawa a yanzu haka, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Suna ganawa ne kan sabanin da ke tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kan tsarin biyan kudi na bai daya wato IPPIS.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a yayin gabatar da kasafin kudi a ranar Alhamis da ta gabata, ya ce ma’aikatan tarayya da aka sanya sunansu a tsarin IPPIS ne kadai za su samu albashi.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, wanda ya jagoranci sauran shugabannin kungiyar zuwa majalisa, ya ce suna ganawar ne domin neman taimakon majalisar dattawan kan ta sanya baki a lamarin, wanda zai zama a madadin IPPIS.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya sha alwashin ladabtar da gurbatattun jami'an SARS, ya ba matasa haƙuri

Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU ta shiga ganawar sirri da shugabannin majalisar dattawa kan IPPIS
Yanzu Yanzu: Kungiyar ASUU ta shiga ganawar sirri da shugabannin majalisar dattawa kan IPPIS Hoto: @premiumTimesng
Asali: Twitter

Ya ce kungiyar ta gana da gwamnatin tarayyar kan madadin IPPIS da ta samar sama da shekaru biyar yanzu, amma babu wani mataki daga gwamnati.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, a yayinda yake jawabi kafin a sallami manema labarai, ya koka kan yadda gwamnatin tarayya ta ki aiwatar da yarjejeniya da dama da ta kulla da kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Zamfara ya rasu

“ina dalilin da za ku kulla yarjejeniyar da kun san ba ku da ikon cika wa?” Lawan ya tambaya.

Har yanzu suna kan ganawa.

A baya mu ji cewa a ranar Juma’a, 9 ga watan Oktoba, 2020, shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce malamai sun shirya kare martabar jami’o’i.

Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana cewa a shirye ASUU ta ke takawa gwamnatin tarayya burki na yunkurin murkushe jami’o’i da ta ke yawan yi.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, ya yi wannan jawabi ne a garin Ibadan, ya na mai maida martani ga jawabin da shugaban kasa ya yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel