Yanzu yanzu: Mazauna Pegi sun rufe kofar ofishin Ministan Abuja, sun fara zanga zanga

Yanzu yanzu: Mazauna Pegi sun rufe kofar ofishin Ministan Abuja, sun fara zanga zanga

- Al'umman Pegi da ke Abuja sun yi zanga-zanga a ma'aikatar birnin tarayya

- A yayin zanga-zangar lumanan, sun mamaye mashigin ofishin ministan birnin tarayya

- Hakan ya biyo bayan sace tsohon mataimakin shugaban hukumar Kuje da wasu da masu garkuwa da mutane suka yi a jiya Lahadi

Mazauna Pegi, wani gari a yankin karamar hukumar Kuje da ke Abuja, a safiyar ranar Litinin, sun rufe kofar ofishin ministan birnin tarayya.

Sun aikata hakan ne a yayinda suke gudanar da zanga-zangar lumana, jaridar The Nation ta ruwaito.

An dai yi garkuwa da tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Kuje, Mista Mohammed Baba da wasu mambobin hukumar a ranar Lahadi.

An tattaro cewa yan bindiga sun yi awon gaba da bas din su a yayinda suke dawowa daga ofishin sabon sakataren ilimi na hukumar, Mista Yunusa Zakari.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Zamfara ya rasu

Yanzu yanzu: Mazauna Pegi sun rufe kofar ofishin Ministan Abuja, sun fara zanga zanga
Yanzu yanzu: Mazauna Pegi sun rufe kofar ofishin Ministan Abuja, sun fara zanga zanga Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar ci gaban garin Pegi, Mista Taiwo Aderibigbe, ya bukaci ministan birnin tarayyar da ya nemo mafita mai dorewa kan sace-sacen mutane da ake yi a yankin.

Aderibigbe ya ce: “matakin da yan sanda ke dauka kan garkuwa da mutane a Pegi bai da tasiri.”

KU KARANTA KUMA: Karon farko: Hadimin Ganduje ya magantu bayan dakatar da shi saboda sukar Buhari

A baya mun kawo cewa yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da yawa a wani hari da suka kai kan al’umman Kuje, Abuja, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kakakin yan sandan birnin tarayya, ASP Yusuf Mariam, ta tabbatar da faruwar al’amarin a ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba.

Ta bayyana cewa ana nan ana kokarin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

An tattaro cewa lamarin ya afku ne da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar, lokacin da mutanen ke dawowa gida bayan sun je taya sabon sakataren ilimi na hukumar, Mista Yunusa Zakari murna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel