Karon farko: Hadimin Ganduje ya magantu bayan dakatar da shi saboda sukar Buhari

Karon farko: Hadimin Ganduje ya magantu bayan dakatar da shi saboda sukar Buhari

- Salihu Tanko Yakasai, hadimin Gwamna Ganduje ya magantu bayan dakatar da shi

- Ganduje dai ya dakatar da hadimin nasa ne saboda sukar shugaba Buhari

- Yakasai ya mika godiya ga abokan arziki da suka kira shi don yi masa jaje

Hadimin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, wanda ya dakatar, Salihu Tanko Yakasai, ya yi martani a karon farko bayan dakatar da shi.

Ganduje dai ya dakatar da Yakasai ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Oktoba sakamakon sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi kan rundunar tsaron SARS.

Yakasai ya mika godiya ga masoya a kan irin kaunar da suka nuna masa bayan labarin dakatarwar nasa ya billo.

Karon farko: Hadimin Ganduje ya magantu bayan dakatar da shi saboda sukar Buhari
Karon farko: Hadimin Ganduje ya magantu bayan dakatar da shi saboda sukar Buhari Hoto: @GuardianNigeria
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun halaka mutum biyu wani hari da suka kai garin Bauchi

Tsohon hadimin na Ganduje a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter ya ce ya ji dadin kulawar da suka nuna masa har cikin zuiyarsa.

“Ina mika godiya ta ga dukkanin mutanen da su ka goya mani baya a jiya, musamman wadanda su ka kira, ko su ka aika mani sakonni ta kafofi dabam-dabam."

“Abin ya yi mani yawa sosai, na yi kokarin mayarwa da kowa martani amma na kasa aikata hakan. Nagode sosai har cikin zuciyata.”

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane masu yawan gaske a Abuja

A wani labarin, Korarren kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa na jihar Kano, Mu'azu Magaji yayi magana akan dakatar da Tanko Yakasai, mai bada shawara na Musamman akan harkokin yada labarai ga Gwamna Ganduje.

Magaji ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda yace an dakatar da Yakasai.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa ranar Lahadi, "Gaskiya ban ji dadin dakatar da Salihu Tanko Yakasai da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi ba.

"Salihu amintacce ne ga Gwamna Ganduje.. Ban ji dadin fitarsa ba. Allah ya zaba masa mafi alkhairi!"

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel