Ahmad ya musanya zargin hannu a dakatar da Mai ba Gwamnan Kano shawara

Ahmad ya musanya zargin hannu a dakatar da Mai ba Gwamnan Kano shawara

- Bashir Ahmaad ya ce bai da hannu a dakatar da Salihu Yakasai daga aiki da aka yi

- Hadimin Gwamnan na Kano ya tsokano fushin Ganduje da sukar gwamnatin tarayya

- Shi ma Kwamishinan da aka tsige kwanaki ya yi magana game da dakatar da Yakasai

A ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba, 2020, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da hadiminsa, Salihu Tanko Yakasai daga aiki.

Wasu sun fito su na zargin wani hadimin shugaba Muhammadu Buhari da hannu a wannan dakatarwar da aka yi wa mai ba gwamnan na Kano shawara.

Hadimin shugaban kasar da ake tuhuma da wannan aiki shi ne Malam Bashir Ahmaad.

Kamar Salihu Yakasai, Malam Bashir Ahmaad ya fito ne daga jihar Kano, kuma ana tunanin ya na da alaka mai kyau da gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje.

KU KARANTA: Mai ba Ganduje shawara ya ragargaji shugaban kasa Buhari

Sai dai Bashir Ahmaad ya yi maza ya karyata wannan zargi da ake yi masa, ya ce sam dai da hannu a matakin da gwamna Ganduje ya dauka kan hadiminsa.

Ahmaad ya ce: “Ban da hannu a abin da ya faru da ‘danuwana, Salihu Tanko Yakasai (Dawisu) kamar yadda wasu su ke rayawa, na ke gani a shafina na Twitter.”

“Abokina ne wanda na ke tare da shi tun ba yau ba, tun tuni na tsawon shekaru.” Inji Ahmaad.

Matashin hadimin shugaban kasar ya karasa jawabinsa a shafin Twitter da cewa: “Za mu cigaba da zama abokai (da Salihu Tanko Yakasai), matukar mu na numfashi.”

KU KARANTA: Ozil da sauran fitattun da su ka taimakawa gwagwarmayar #EndSARS

Ahmaad ya musanya zargin hannu a dakatar da Mai ba Gwamnan Kano shawara
Bashir Ahmaad da Dawisu Hoto: Newspot
Asali: UGC

Shi ma Yakasai ya fito ya yi magana dazu, ya ce:

“Ina mika godiya ta musamman ga duka mutanen da su ka mara mani baya a jiya, musamman wadanda su ka kira, ko su ka aika sakonni ta kafofi dabam-dabam."

“Abin ya mani yawa, na yi kokarin maidawa kowa amsa, amma ban iya ba. Nagode sosai, har daga karkashin zuciyata.” - @Dawisu, 12 ga watan Oktoba, 2020.

Dazu kun ji cewa Kwamishinan da Mai girma gwamna ya tsige ya yi magana game dakatar da Salihu Yakasai da aka yi daga aiki saboda sukar shugaban kasa.

Mua'zu Magaji wanda ya rasa kujerarsa a irin wannan dalili bai ji dadin dakatar da Yakasai ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel