Jami’ar As-Salam: Gwamnonin Arewa 5 sun hada N250m inji Gwamna Badaru

Jami’ar As-Salam: Gwamnonin Arewa 5 sun hada N250m inji Gwamna Badaru

- Jama’atul Izalatul Bidi’a Waikamatul Sunnah za ta kafa jami’ar addini

- Kungiyar Izala ta kaddamar da shirin wannan aiki a jihar Jigawa a jiya

- Gwamnoni da ‘Yan Majalisa sun taimaka da gudumuwar Miliyan 400

A ranar Lahadi, 11 ga watan Oktoba, 2020, aka kaddamar da shirin aikin gina jami’ar Assalam Global University a garin Hadejia, jihar Jigawa.

Kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi'a; a Waikamatul Sunnah (JIBWIS), wanda aka fi sani da Izala ce ta ke kokarin gina jami’ar musulunci a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto, ta bayyana irin gudumuwar da aka tara wa kungiyar addinin.

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara ya ba JIBWIS N100m domin gina Jami’a?

Jama’atul Izalatul Bidi'a Waikamatul Sunnah ta samu kudi ya kai Naira biliyan daya daga hannun gwamnonin jihohi. ‘yan majalisa, da wasu ‘yan siyasa.

Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya sanar da cewa takwarorinsa na Kano, Sokoto, Kebbi da Katsina sun bada gudumuwar miliyan 250.

Haka zalika an samu wani Bawan Allah da ya ki bari a bayyana sunansa da ya ba kungiyar addinin kudi har Naira miliyan 500 inji gwamnan na Jigawa.

‘Yan majalisa sun hadu sun bada gudumuwar Naira miliyan 150. Bayan haka tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu ya taimaka da miliyan 10.

KU KARANTA: Kwamitin Jami'ar As-Salam, ya kammala aikin shirye-shirye

Jami’ar As-Salam: Gwamnonin Arewa 5 sun hada N250m inji Gwamna Badaru
Taron kaddamar da aikin Jami’ar As-Salam Hoto: DailyTrust
Asali: UGC

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi jawabi a wajen taron, ya ce sun kafa jami’ar ne domin masu tasowa su samu ilmin zamani, game da na musulunci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu wakilcin Ministan sadarwa, Dr. Ibrahim Ali Pantami, wanda ya yi jawabi a madadin shugaban kasar.

Mai alfarma Sultan, Sa’ad Abubakar, wanda ya kaddamar da shirin ya yi amfani da wannan dama wajen tunatar da ‘yan siyasa lahira domin su ji tsoron Allah.

Tun ba yau ba ku ka ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta ba kungiyar Izalatul Bid’a waikamatus Sunnah kyautar shekta 65 na fili domin ta gina jami'a.

Kungiyar ta zabi Jigawa ne saboda zaman lafiyan jihar, da kusancinta da Arewa maso gabas.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng