Atisayen Sahel Sanity: Dakarun soji sun kakkaɓe ƴan ta'adda a shiyyar Arewa maso Yamma
- Rundunar Operation Sahel Sanity na ci gaba da karfafa ayyukanta inda take ci gaba da kutsawa yankunan karkara don farautar yan ta’adda
- Dakarun sojin sun yi nasarori da dama kan yan fashi da makami a yankin arewa maso yamma
- Sun halaka wasu yan bindiga sannan suka samo makamai tare da ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su
Yayinda ake shirin shiga yanayi na bazara a yankin arewa maso yamma, rundunar Operation Sahel Sanity ta karfafa ayyuka inda take ci gaba da kutsawa yankunan karkara don farautar yan ta’adda.
Hakazalika a tsakanin ranakun 4 zuwa 9 ga watan Oktoba, rundunar hadin gwiwa ta Operation Sahel Sanity da na Operation Hadarin Daji sun yi aikin kakkaba.
Sun yi aikin ne domin gano mafakar yan bindiga a kananan hukumomin Dankar, Kandawa, Yau yau, Hayin Yau yau, Bugaje, Zandam, Kwari Mai Zurfi, Yar Gamji, Bukuru da Jaiabaiya a kananan hukumomin Batsari da Jibiya na jihar Katsina.
Hakan ya yi sanadiyar kashe yan bindiga uku, yayinda sauran suke tsere da raunuka sakamakon harbin bindiga.
KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kai wa masu zanga-zangar a ruguza rundunar SARS hari a Abuja
Bayan arangamar, dakarun sojin sun samo mujallar bindigar AK 47 dauke da harsasai da bindiga mallakar yan bindigan.
Har ila yau sun kuma lalata babur da mafakar yan bindiga takwas a aikin wanda ke ci gaba da gudana.
A wani aiki da dakarun suka gudanar, an kama yan bindiga hudu a kauyukan Kankara da Tudu a karamar Katsina ciki harda wani shugaban yan ta’adda mai suna Mujitafa Shehu.
A wani ci gaba, a ranar 5 ga watan Oktoba, rundunar a Operation Base Bena a karamar hukumar Wasagu-Danko da ke jihar Kebbi, tare da rundunar Bataliya 223 da aka tura Wasagu da Unashi, sun ceto mutum biyu da aka yi garkuwa da su.
Sun yi nasarar ne a yayin wata kakkaba da suka yi don gano mafakar yan bindiga a kauyukan Dan Umaru, Rancho da Dan Duniya.
Tuni aka sada wadanda aka ceto ga yan uwansu yayinda mazauna yankin suka cika da murna.
KU KARANTA KUMA: Ba ma yi: Mutane 100,000 sun yi wa Buhari tawaye a shafukansu na Twitter
A wannan rana kuma, dakarun Operation Base Jengebe sun kama wani mai fatauci miyagun kwayoyi, Mubarak Shehu a yankin Wanki da ke karamar hukumar Gusau.
An kama mai laifin dauke da pakiti 20 na alluran Pentazocine a babur dinsa yayinda yake a hanyarsa ta kai kayan kauyen Kungurmi da ke karamar hukumar Bungudu.
Binciken farko ya nuna cewa mai fataucin kwayoyin ya kasance mamba na kungiyar da ke kai wa yan bindiga miyagun kwayoyi a daji.
A wani lamari makamancin haka, a ranar 6 ga watan Oktoba, dakarun da aka tura Yar Santa a karamar hukumar Kankara sun ceto wata mace da aka yi garkuwa da ita a yankin.
An kuma sada ta da yan uwanta.
Dakarun sun kuma kai mamaya sannan suka lalata sansanin yan bindiga a lokacin wata kakkaba da suka yi.
Sun yi aikin kakkaban ne a Garin Inu, dajin Shekewa, Jajaye, Kerewa, Solar, Mallamawa da Gobirawa a jihar Katsina.
KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kai wa masu zanga-zangar a ruguza rundunar SARS hari a Abuja
Kayayyakin da aka samo sun hada da bingigogi biyu da kayayyaki daban-daban.
A ranar 9 ga a watan Oktoba, rundunar da aka tura Operation Base Magami yayinda suke martani ga wani kira mai cike da damuwa, sun ceto mutum 23 da aka yi garkuwa da su.
Yan bindiga ne suka yasar da su a lokacin da suke tserewa dakarun da suka tunkaro mafakarsu a hanyar Zauni-Jengebe da ke karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.
Bincike ya nuna an yi garkuwa da mutanen ne yayinda suke a hanyarsu ta zuwa kasuwar Magami daga Gusau a cikin wata motar bas.
KU KARANTA KUMA: Ku yi rayuwa mai kyau, ko za ku samu makoma kyau - Obasanjo ya shawarci 'yan Najeriya
Duk an mika su ga yan uwansu yayinda ake kokarin gano mambobin kungiyar ta’addancin, hedkwatar tsaro ta bayyana.
A wani labari na daban, Sufeta Janar na Rundunar 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da soke runduna ta musamman mai yaki da fashi da maki wato SARS.
Ya ce za a tura jami'an da ke tsohuwar rundunar ta SARS zuwa wasu rundunonin na musamman na 'yan sandan.
Wannan na dauke ne cikin wata jawabi da ya yi kai tsaye a ranar Lahadi 11 ga watan Oktoban 2020.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng