Yan sanda sun kai wa masu zanga-zangar a ruguza rundunar SARS hari a Abuja

Yan sanda sun kai wa masu zanga-zangar a ruguza rundunar SARS hari a Abuja

- Jami'an rundunar yan sandan Najeriya sun tarwatsa dandazon masu zanga-zangar a ruguza rundunar SARS a Abuja

- Sun yi hakan ne ta hanyar amfani da harsasai, ruwan zafi da barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zangar

- Lamarin ya afku ne a yau Lahadi, 11 ga watan Oktoba

Rundunar yan sanda ta tarwatsa dandazon masu zanga-zanga da harsasai, ruwan zafi da barkonon tsohuwa a Abuja.

Masu sanya-zangar na neman a kawo karshen cin kashin da rundunar yan sanda ke yi wa jama’a.

Sannan suna kira ga ruguza rundunar SARS wacce ke take yancin dan adam.

Yan sanda sun kai wa masu zanga-zangar a ruguza rundunar SARS hari a Abuja
Yan sanda sun kai wa masu zanga-zangar a ruguza rundunar SARS hari a Abuja
Asali: Original

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Akeredolu ya lallasa Jegede, Ajayi da sauransu da tazarar kuri'u 53,380 a kananan hukumomi 14

Adebayo Raphael, jagoran cibiyar yanci, ya bayyana yadda lamarin ya afku a ranar Lahadi.

“Ya yan uwa yan Najeriya, yanzun nan aka bada mana barkonon tsohuwa. An lalata mani madubin idona. An harbi wani a keyarsa,” in ji shi.

“Sun yi amfani da barkonon tsohuwa. Kai tsaye suka harbe mu, sannan suka yi amfani da motar ruwan zafinsu.”

A ranar Asabar ma, yan sandan sun far ma masu zanga-zanga wadand suka kewaye hedkwatar rundunar a Abuja domin neman a kawo karshen SARS.

A halin da ake ciki, mun ji cewa Sufeta Janar na Rundunar 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da soke runduna ta musamman mai yaki da fashi da maki wato SARS.

Ya ce za a tura jami'an da ke tsohuwar rundunar ta SARS zuwa wasu rundunonin na musamman na 'yan sandan.

Wannan na dauke ne cikin wata jawabi da ya yi kai tsaye a ranar Lahadi 11 ga watan Oktoban 2020.

Sanarwar na zuwa ne bayan al'umma sun shafe kwanaki suna zanga-zanga a tituna da kuma dandalin sada zumunta na neman a soke rundunar a kasar baki daya don kisa da cin zarafin al'ummma da suke yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel