Kasafin kudi: Buhari da Osinbajo sun ware N3.2bn domin tafiye-tafiye zuwa ketare a 2021

Kasafin kudi: Buhari da Osinbajo sun ware N3.2bn domin tafiye-tafiye zuwa ketare a 2021

- A ranar Alhamis ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2021

- Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudi N13.1trn a gaban mambobin majalisar tarayya yayin wani zama na musamman

- Buhari ya bayyana cewa annobar korona da faduwar farashin danyen mai ta nakasa tattalin arzikin Najeriya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, sun ware N3.2bn a cikin kasafin kudin 2021 domin tafiye-tafiye.

A ranar Alhamis ne shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2021 a gaban majalisar tarayya.

A ranar Juma'a ne ofishin kasafi ya fitar da bayanai dalla-dalla a kan kasafin da shugaba Buhari ya gabatar.

A cikin bayanin, Buhari ya nuna cewa zai kashe N2.426bn a tafiye-tafiye na cikin gida da na waje.

Daga cikin, Buhari zai kashe N1.651bn a tafiye-tafiye zuwa ketare yayin da zai kashe N775.602 a tafiye-tafiye na cikin gida.

DUBA WANNAN: Zaben gwamna: An bukaci dukkan gwamnoni su gaggauta fita daga jihar Ondo

Kazalika, Buhari zai kashe N4.135n a matsayin kudin gudanar da al'amura a fadar gwamnati.

A karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa, an ware ma sa N1.079bn a matsayin kudin gudanar da al'amura a fadarsa.

Kasafin kudi: Buhari da Osinbajo sun ware N3.2bn domin tafiye-tafiye zuwa ketare a 2021
Buhari da Osinbajo
Asali: UGC

Mataimakin shugaban kasa zai kashe N517.060m a tafiye-tafiye zuwa ketare yayin da zai kashe N283.974m a tafiye-tafiye na cikin gida.

A ranar Alhamis ne shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudi na N13.1trn yayin wani zama na musamman da ya hada mambobin majalisar dattijai da na wakilai wuri guda.

DUBA WANNAN: Ta nan kudade su ke zirarewa: Majalisa ta shawarci Buhari ya soke wasu hukumomi

Shugaba Buhari ya bayyana cewa bullar annobar korona ya taba tattalin arzikin Najeriya, sannan ya kara da cewa faduwar farashin danyen mai ta hana gwamnati samun isassun kudin shiga.

Buhari ya gabatar da kasafin kudi na N13.1trn, hakan ya nuna cewa an samu karin kaso 20% a kan adadin kudin da gwamnati ta yi kasafi a baya.

A cewar Buhari, akwai gibin N4.8trn a cikin kasafin, wanda ya bayyana cewa gwamnati za ta cike gibin da rance daga ketare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayarku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel