An kashe dan sanda daya a yayin da zanga-zangar neman rushe SARS ta rikide zuwa rikici a wasu jihohi 3
- 'Yan Najeriya na cigaba da nuna fushinsu tare da neman gwamnati ta soke rundunar 'yan sandan SARS da aka kafa domin yaki da fashi da makami
- Ma su neman a soke SARS su na zargin jami'an rundunar da aikata laifukan da aka kafasu domin su yaka
- A yayin da aka shiga rana ta biyu da fara gudanar da zanga-zanga a wasu jihohi, an samu barkewar rikici tsakanin jami'an tsaro da fararen hula
An samu barkewar rikici a Abuja, Delta, da Osun yayin zanga-zangar neman a kawo karshen 'yan sandan SARS da kuma nuna kyamar zaluncin jami'an 'yan sanda.
Jaridar Punch ta rawaito cewa 'yan sanda sun yi harbe-harbe domin tarwatsa ma su zanga-zangar.
A Osogbo, babban birnin jihar Osun, zanga-zangar ta haddasa cunkuso a babbar kwanar Ola-Iya.
Rahotanni sun bayyana cewa ma su zanga-zanga sun yi ruwan duwatsu a kan jami'an 'yan sandan da ke kokarin hanasu cigaba da gudanar da tattakin da suka fara.
DUBA WANNAN: Sojoji sun yi 'caraf' da mai safarar makamai ga kungiyar Boko Haram daga ketare
Jaridar TheCable ta rawaito cewa an kashe wani dan sanda, Etaga Stanley, mai mukamin kofur, yayin zanga-zanga a jihar Delta ranar Alhamis.
Mutane da dama da suka hada da jami'an 'yan sanda sun samu raunuka yayin zanga-zangar.
TheCable ta ce babu wani bayani sahihi dangane da dalilin kisan dan sandan, wanda aka samu gawarsa a yashe cikin kaskanci a kan wani titi da ke Delta.
DUBA WANNAN: Rashin imani: An kone dan Najeriya 'kurmus' da ransa a kasar Libiya
Sai dai, babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Muhammed Adamu, ya ce ba za su yarda da cin zarafin jami'an 'yan sanda da sunan zanga-zanga ba.
'Yan Najeriya sun dade su na guna-guni tare da yin kiraye a kafafen yada labarai da na sada zumunta a kan a rushe rundunar SARS.
Jama'a na cigaba da bayar da shaidar yadda jami'an SARS su ka zaluncesu ko cin zarafin wani nasu duk da kasancewar aikin jami'an tsaro shine kare lafiya da dukiyar 'yan kasa nagari, ma su bin doka.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayarku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng