Kasafin kudi: Buhari ya bayyana dalilin karin kudin fetur da lantarki

Kasafin kudi: Buhari ya bayyana dalilin karin kudin fetur da lantarki

- A jiya Shugaban kasa ya gabatar da kasafin kudin shekarar badi a Majalisa

- Muhammadu Buhari ya yi karin haske game da tashin farashin wuta da mai

- Alamu sun nuna gwamnatin Buhari ba za ta lashe amai kan karin da ta yi ba

Yiwuwar rage kudin shan wutar lantarki da kudin fetur ya dushe bayan shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kundin kasafin shekarar 2021.

Jaridar Guardian ta bayyana cewa kasafin kudin da shugaban kasa ya gabatar ya nuna cewa babu maganar biyan tallafin man fetur a shekara mai zuwa.

A cikin kasafin kudin Naira tiriliyan 13.08 da gwamnatin tarayya ta yi, ba a yi maganar biyan ‘yan kasuwa kudin tallafin mai domin saukar da farashi ba.

KU KARANTA: Buhari zai aro Naira Tiriliyan 4.8 a kasafin kudin shekara mai zuwa

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan kungiyoyin kwadago sun dakatar da zuwa yajin aiki da nufin cewa gwamnati za ta janye karin da ta yi a wuta da mai.

Shugaban ya ce barin farashin man fetur a hannun ‘yan kasuwa zai taimakawa gwamnatinsa wajen yin wasu muhimman abubuwa da dukiyar kasa.

Haka zalika Mai girma Muhammadu Buhari ya ce karin farashin shan wutar lantarki ya zama dole ne domin biyan bashin da ya yi katutu a harkar wutar.

Ga abin da Buhari ya fadawa ‘yan majalisa a jiya: “Sabon farashin man fetur ya bada damar a samu rarar kudin da ake kashewa wajen biyan tallafin mai.

KU KARANTA: Abin da kasafin da Shugaba Buhari ya gabatar ya kunsa

Kasafin kudi: Buhari ya bayyana dalilin karin kudin fetur da lantarki
Shugaba Buhari Hoto: Twitter/Bashir Ahmaad
Asali: Twitter

“Yayin da sauyin da aka gani a harkar wutar lantarki zai taimaka wajen maganin bashin da ke cikin harkar.”

Jaridar ta ce shugaban kasar bai yi wa majalisar tarayya bayanin inda za a samo kudin da za a kara wa ma’aikata albashi kamar yadda ya yi alkawari kwanan nan.

A ranar Malamai ta Duniya, Ministan ilmi, Adamu Adamu, ya bada sanarwar gwamnati za ta kara albashin malaman makarnata, tare da kara masu shekarun aiki.

Ministan ilmin ya ce shugaban kasa ya kara wa malamai shekarun aiki daga 35 zuwa 40.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng