PTF ta ce komawa bakin aiki gadan-gadan zai iya sa alkaluman COVID-19 su tashi

PTF ta ce komawa bakin aiki gadan-gadan zai iya sa alkaluman COVID-19 su tashi

- Babu mamaki a ga karuwar masu dauke da Coronavirus a ‘yan kwanakin nan

- Gwamnati ta bada umarnin bude makarantu bayan jiragen sama sun dawo aiki

- PTF ta ce a dalilin haka, cutar COVID-19 za ta iya kara bazuwa a cikin Najeriya

A ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba, kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar COVID-19, ya yi magana game yiwuwar karuwar cuta.

Kwamitin na PTF sun yi zama a jiya, inda su ka bayyana cewa komawa bakin aiki da bude tattalin arziki da aka yi, zai iya jawo alkaluma su tashi.

Ministan lafiya na kasa, Dr. Osagie Ehanire, ya yi kira ga jama’a cewa ka da su yi sanya wajen daukar matakan kare kai daga kamuwa da Coronavirus.

KU KARANTA: COVID-19 ta harbi mutane 155 a rana daya - NCDC

Osagie Ehanire ya ce ganin an bude kasuwanni da filayen tashi da saukar jirgin sama da kuma makarantu, akwai yiwuwar COVID-19 ta kara bazama sosai.

Ministan ya ke fadawa manema labarai a Abuja: “Mun damu da karuwar masu cuta da ake samu a sauran kasashen da a da ba a samun yaduwar cutar sosai.”

Ya ce: “Wannan ya sa dole a maida hankali cewa za a iya samun karuwar masu dauke da cutar idan ba mu dauki matakan da su ka dace na gwaji da kula ba.”

Ehanire ya yi kira ga mutane su guji tafiye-tafiyen da ba su zama dole ba a wannan yanayi da aka ciki, musamman zuwa wuraren da ake da yawan masu cutar.

KU KARANTA: Mahaifiyar Mataimakin Gwamnan Adamawa ta mutu a shekara 118

PTF ta ce komawa bakin aiki gadan-gadan zai iya sa alkaluman COVID-19 su tashi
Ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire Hoto: Nairametrics
Asali: UGC

Bayan haka, Ministan ya koka da karancin gwajin da ake yi a Najeriya, ya ke cewa adadin mutanen da ake yi wa gwaji a rana ya yi kasa da abin da ya kamata a yi.

“Za mu iya yi wa mutane 3, 500 gwai a kullum, amma abin da mu ke samu a rana bai kai haka ba. Wannan ya sa abokan hulda su ka fara kokwanton alkalumanmu.”

Ku na da labari cewa hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya, NCDC, ta bayyana cewa cutar COVID-19 ta harbi mutane 103 a ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba, 2020.

Jihohin da aka samu cutar sun hada da: Legas, Ribas, Oyo, Kaduna, Bauchi, Kano da sauransu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel