Gaskiya da gaskiya: Pantami ya bayyana gatan da FG za ta yi wa mazauna IDPs ta hannun ma'aikatarsa

Gaskiya da gaskiya: Pantami ya bayyana gatan da FG za ta yi wa mazauna IDPs ta hannun ma'aikatarsa

- Ana yawan samun rahoton almundahana da badakala wajen rabawa mazauna IDPs kayan tallafi

- Minstan sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami, ya dauki alkawarin cewa za a samar da lambobi na musamman ga mazauna IDPs

- A cewar Ministan, bawa mazauna IDPs lambobin zai bawa gwamnati damar ba su tallafi kai tsaye

Gwamnatin tarayya (FG) ta yi alkawarin samar da lambobi na musamman ga kowanne mazaunin sansanin 'yan gudun hijira (IDPs) da ke fadin kasar nan.

Ministan sadarwa da sabon tsarin gina tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani, Dakta Isa Ali Pantami, ne ya sanar da hakan yayin rantsar da kwamitin mutane 14 domin rabon kayan tallafi a Abuja.

A cewar ministan, gwamnatin tarayya za ta samar da lambobi na musamman ga mazauna IDPs domin samun saukin raba mu su kayan tallafi kai tsaye.

Dakta Pantami ya bayyana cewa hukumar bayar da katin dan kasa (NIMC) aka dorawa alhakin samar da lambobin ga mazauna IDPs.

KARANTA: Tattalin arzikin Najeriya zai iya 'komawa gidan jiya' a karo na biyu cikin shekaru 4 - Buhari

Ministan ya ce ma'aikatarsa za ta raba kayan tallafi ga 'yan Najeriya domin rage musu radadin matsin da aka shiga sakamakon bullar annobar korona.

"Tun a ranar 1 ga watan Mayu na umarci ma'aikatu da hukumomin da ke karkashina su samar da kayayyakin da za a rabawa 'yan Najeriya domin rage musu radadin bullar annobar korona.

Gaskiya da gaskiya: Pantami ya bayyana gatan da FG za ta yi wa mazauna IDPs ta hannun ma'aikatarsa
Pantami ya yin wani taron FEC
Asali: Twitter

"Sun yi biyayya, sun samar da kayayyakin da za mu fara rabawa yau," a cewarsa.

Hukumomin da su ka samar da kayan tallafin sun hada da NCC, NITDA, Galaxy Backbone Ltd, NigComSat, da NIPOST.

A ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa Dakta Pantami, ya yabawa kokarin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

KARANTA: Wata Sabuwa: Trump ba Kirista bane - Fafaroma ya yi 'fashin baki'

A cewar ministan, shugaba Buhari ya taimaka matuka wajen saka Najeriya a sahun gaba a cikin kasashen nahiyar Afrika da duniya da su ke taka rawar gani a bangaren fasahar zamani.

Ministan ya jinjinawa shugabancin Buhari a kan kokarin dora Najeriya a kan tafarkin cigaba duk da tsaikon da tattalin arziki ya samu saboda ballewar annobar korona.

Pantami ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban hukumar NITDA, Mallam Kashifu Inuwa, wanda ya wakilce shi a wurin wani taro da aka shirya a Abuja.

Wata cibiya ce mai suna 'Innovation Hub Africa' ta shirya taron mai taken 'Nigeria Innovation Summit 2020' wanda aka yi ranar Talata a Abuja.

"Mu, a Najeriya, mun yi dace da shugabanci a irin wannan lokaci. Gwamnatin kasa, a karkashin jagorancin shugaba Buhari, ta saka tubalin cigaban Najeriya tun kafin bullar annobar korona," a cewar wani bangare na jawabin Pantami da Inuwa ya karanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng