Harin zaben 2023: Atiku ya gana da Kwamitin ɗinke ɓarakar PDP (hotuna)

Harin zaben 2023: Atiku ya gana da Kwamitin ɗinke ɓarakar PDP (hotuna)

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gana da mambobin kwamitin ɗinke ɓaraka ta PDP

- Jagoran kwamitin kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ne yayi masu jagora a yau Laraba, 8 ga watan Oktoba

- Atiku ya bayyana cewa sun tattauna yadda za su farfado da jam’iyyar PDP

Mambobin kwamitin sulhu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Laraba, 8 ga watan Oktoba, sun gana da tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP ne ya kafa wannan kwamitin domin ganin yadda PDP za ta habbaka nasarorinta da farfado da kanta a kasar kafin zaben 2023.

Shugaban kwamitin kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ne ya yi masu jagora kamar yadda tsohon mataimakin shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA KUMA: Zulum ya zauna a sashen talakawa na jirgin sama, ya dauki hoto da jama'a

Harin zaben 2023: Atiku ya gana da Kwamitin ɗinke ɓarakar PDP (hotuna)
Harin zaben 2023: Atiku ya gana da Kwamitin ɗinke ɓarakar PDP Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Atiku ya ce sun tattauna da kwamitin cikin nasara inda ya fada masu nashi dabarun game da yadda za su farfado da jam’iyyarsu tare da karfafa ta.

Ya wallafa: “Yanzun nan n agama ganawa tare da kwamitin ɗinke ɓaraka ta PDP karkashin jagorancin Gwamna @SenBalaMohammed kan yadda za mu karfafa jam’iyyarmu. Taron ya kasance cike da nasara sannan na baiwa tawagar nawa shawarwarin na farfado da ita.”

KU KARANTA KUMA: Gidajen Katsina da Barebari sun kai wa sabon Sarkin Zazzau gaisuwar ban-girma

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Mista Ayodele Peter Fayose ya jefi wasu jiga-jigan PDP da laifin hannu a harin da aka kai masa a jihar Ondo.

Ayodele Fayose ya ambaci sunan tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa, Cif Bode George cikin wadanda su ka kitsa harin da aka kai masa.

Fayose ya ce akwai hannun mai girma gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, a yunkurin ci masa mutunci da aka yi a babban gangamin PDP.

Tsohon gwamnan na PDP ya fitar da jawabi ta bakin hadiminsa, Lere Olayinka, ya na mai cewa duk da abin da ya faru, ba zai daina fadin gaskiya ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel