Gwamnatin Buhari za ta kafa masana'antun kera takalma da suturu na bilyoyin Naira a Kano da Aba

Gwamnatin Buhari za ta kafa masana'antun kera takalma da suturu na bilyoyin Naira a Kano da Aba

- Gwamnatin tarayya za ta kafa masana’antun kera takalma, sutura da sarrafa leda a jihohin Kano da Abia

- Ana sanya ran shirin zai kasance karkashin yarjejeniyar hadin-gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu

- An kiyasta cewa aikin zai samar da akalla ayyuka 4,330 ga yan Najeriya

Majalisar zartarwa ta amince da kafa masana’antu biyu na kera takalma, sutura da sarrafa leda a Janguza, jihar Kano da Aba a jihar Abia karkashin shirin hadin-gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan, bayan taron majalisar zartarwa karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Rikici ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a Lagas

Ministan ya bayyana cewa kamfanin Najeriya ce za ta kula da aikin tare da taimakon hadin-gwiwa daga China.

Gwamnatin Buhari za ta kafa masana'antun kera takalma da suturu na bilyoyin Naira a Kano da Aba
Gwamnatin Buhari za ta kafa masana'antun kera takalma da suturu na bilyoyin Naira a Kano da Aba Hoto: @DailyPostNGR
Asali: UGC

A cewarsa, kwangilar zai samar da kimanin ayyuka 4,330 baya ga kudaden hannun jari da suka kai kimanin naira biliyan 5.1, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

“A saboda haka, idan yarjejeniyar ta kullu, za a samu alfanu masu tarin yawa. Kimanin mutane 1,330 za su samu aiki kai tsaye, yayinda kimanin mutane 3,000 za su samu aiki a kaikaice.

“Amfanin haka baya ga samun aiki da yan Najeriya za su yi shine samun damar horar da fursunoni da ke a gidajen gyaran halayyanmu a Janguza, jihar Kano da Aba a jihar Abia.

KU KARANTA KUMA: Rashin albashi mai kyau ne ke sa alkalai aikata rashawa – Majalisar dattawa

“An bayar da kwangilar satifiket na cikakken horon kasuwanci ga kamanin Messrs LG Investment Limited, wata kamfanin Najeriya wacce ke da hadin gwiwa da kamfanin kasar China, Full Technology Incorporated daga Beijing, China.”

A gefe guda, Shugaba Muhammadu ya fara jawabinsa na gabatar da kasafin kudin 2021 da mika godiya ga yan Najeriya bisa hakuri, jajircewa da goyon bayan da suka cigaba da nunawa gwamnatinsa duk da halin kuncin da ake ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng