Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya ya gurfanar da Ikedi Ohakim a gaban kotu

Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya ya gurfanar da Ikedi Ohakim a gaban kotu

- IGP ya maka tsohon Gwamna Ikedi Ohakim a gaban wani kotu a Abuja

- Ana zargin tsohon Gwamnan kasar da laifin damfarar wata mata a 2019

- Bayan haka ana tuhumar Ohakim da laifin karya da sunan Raji Fashola

Sufetan ‘Yan sandan Najeriya na kasa, ya shigar da karar tsohon gwamnan jihar Imo, Ikedi Ohakim, a wani babban kotun tarayya da ke Abuja.

Shugaban ‘yan sandan ya na zargin tsohon gwamnan da laifuffuka uku da su ka hada da sata da kuma amfani da sunan wani wajen yaudarar mutane.

Ikedi Ohakim ya rike kujerar gwamna a jihar Imo tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011. Ohakim ya sake neman takara a zaben 2019, amma bai yi nasara ba.

KU KARANTA: NDLEA ta rusa gonar tabar wiwi a Kogi

Ana zargin tsohon gwamnan na Imo ya yi amfani da sunan Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya fake da cewa ya mallaki wani fili a Legas.

TheNigeriaLawyer ta ce ‘Yan sanda sun shigar da wannan kara ne mai lamba CR/993/2020 ta ofishin IGP a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, 2020.

Masu shigar da karar su na tuhumar Ohakim da yin karya a bayanin da ya ba ‘yan sanda na cewa ya ba wata Chinyere Lilian Amuchienwa Miliyan 100.

Tsohon gwamnan bai iya gaskata ikirarin da ya ke yi na cewa ya ba wannan Baiwar Allah kudi a lokacin yakin neman zabensa a shekarar da ta wuce ba.

KU KARANTA: Zaben Ondo: Rabiu Kwankwaso ya tara gangamin ‘Yan Arewa a kamfe

Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya ya gurfanar da Ikedi Ohakim a gaban kotu
Ikedi Ohakim Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Stanley Nwodo ya sa hannu a wannan kara inda ya bayyana cewa Ohakim ya fadawa ‘yan sanda cewa Chinyere Amuchienwa ta yi barazanar kashe shi.

Karya da tsohon gwamnan ya yi ta sabawa sashe na 140 dokar laifi a Arewacin Najeriya na 1968.

Bayan haka Ohakim ya damfari wannan mata cewa ya na da filin saidawa a garin Ikeja bayan ya tabbatar da cewa bai da mallakin wani fili da ya ke magana.

A jiya ku ka ji cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da gyaram titin jirgin kasan da ya ratsa Maiduguri zuwa garin Fatakwal.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana haka bayan an fito daga taron FEC na makon na.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel