Okonjo-Iweala da Myung Hee sun zarce zuwa matakin zaben karshe a WTO

Okonjo-Iweala da Myung Hee sun zarce zuwa matakin zaben karshe a WTO

- Mutumiyar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ta kai matakin karshe a zaben WTO

- Ngozi Okonjo-Iweala za ta gwabza da Ministar kasar Koriya, Yoo Myung Hee

- A shekarar nan ne kungiyar WTO za ta samu shugaba mace ta farko tun 1995

Jaridar Bloomberg ta fitar da rahoto cewa kungiyar WTO ta kasuwancin Duniya ta yanke hukunci game da takarar da za ayi wannan shekarar.

A ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, 2020, WTO ta zabi sunayen ‘yan takarar da za su gwabza a zaben karshe; daga ciki har da ‘Yar Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Ngozi Okonjo-Iweala da kuma Yoo Myung Hee ne su ka samu kai wa matakin karshe na wannan zabe a Geneva.

KU KARANTA: Dangote ya na goyon bayan Okonjo-Iweala a zaben WTO

Misis Myung Hee mai shekaru 53 ce Ministar kasuwanci ta kasar Koriya ta Kudu. Myung Hee ce mace ta farko da ta rike wannan kujera a kasarta.

Myung Hee ta yi kokari wajen bunkasa karfin tattalin arzikin Koriya, a lokacin ta ne kasar ta shiga yarjejeniya da irinsu kasashen Birtaniya da Amurka.

Ngozi Okonjo-Iweala mai shekaru 66 a Duniya ta rike kujerar Ministar kudi sau biyu a Najeriya, ta yi aiki har a babban bankin Duniya a matsayin Darekta.

Jaridar ta ce a yau ake sa ran cewa shugaban majalisar WTO, David Walker zai sanar da sakamakon zaben da aka kada a zagayen da ya gabata.

KU KARANTA: Kasar Benin za ta goyi bayan Ngozi Okonjo-Iweala a kujerar WTO

Okonjo-Iweala da Myung Hee sun zarce zuwa matakin zaben karshe a WTO
Okonjo-Iweala Hoto: Twitter/NOIweala
Asali: Twitter

‘Yan takara uku sun sha kasa a wannan mataki na daf da karshe: ‘yan takarar su ne: Liam Fox, Amina Jibril, da kuma Mohammad Al-Tuwaijri.

Tun da aka kafa WTO a Duniya, mace ba ta taba zama shugabanta ba, watakila sai a bana za a dace bayan nasarar Okonjo-Iweala da takwararta.

A ranar Litinin mu ka kawo maku labari cewa alamun sun nuna Ngozi Okonjo-Iweala za ta iya zuwa mataki na gaba a takarar kungiyar WTO.

Tsohuwar Ministar tattalin ta yi aiki da gwamnatin Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel