Da aka je aka dawo Ambasada Ahmad Bamalli ya zama sabon Sarkin Zazzau

Da aka je aka dawo Ambasada Ahmad Bamalli ya zama sabon Sarkin Zazzau

- Gidan Mallawa sun doke Bare-bari da Katsinawa a wajen samun sarautar

- Kafin ayi wannan nadi a jiya, an yi ta kai ruwa-rana, ana ta jita-jita iri-iri

- A lokacin da Sarkin Zazau ya rasu, Ambasada Ahmed Bamalli ba ya kasar

Bayan shekaru 17 da rasuwar Sarki Alhaji Shehu Idris, gwamnatin Nasir El-Rufai ta sanar da Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarki.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto na yadda aka yi Magajin Garin Zazzau ya gaji kasar ta Zazzau.

Tsohon Magajin Garin na Zazzau amini ne na Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, har kuma ya taba yin aiki da gwamnatinsa.

Ana zargin Nasir El-Rufai ya yi watsi da sakamakon zaben da masu zaben sabon Sarki su ka yi, ya bukaci su sake yin wani sabon zaben a makon jiya.

KU KARANTA: Bamalli ya zama Sarkin farko daga gidan Mallawa bayan shekara 100

A sunayen ‘yan takara na farko da aka kai gaban gwamnan Kaduna, babu sunan Ahmed Nuhu Bamalli, don haka gwamna ya ki karbar sunayen.

Gwamnati ta fake da cewa an cire sunayen ‘yan takara biyu; Bunu Zazzau da Sarkin Dajin Zazzau Don haka ta ce a sake shirin zaben Sarkin tun daga farko.

Manyan masu neman kujerar su ne: Iyan Zazzau, Bashar Aminu, Yariman Zazzau, Muhammed Munnir Jafaru da Turakin Zazzau, Aminu Shehu Idris.

Daga nan ne labari ya fara canzawa, masu zaben sarkin su ka yi watsi da matakin farko da su ka dauka inda Iyan Zazzau, Bashir Aminu ya zo na farko a zabe.

KU KARANTA: Wanene Sarki Ahmad Bamalli, wanda ya karya tarihin shekaru 100 a Zazzau

Da aka kai aka dawo Ambasada Ahmad Bamalli ya zama sabon Sarkin Zazzau
Ahmed Nuhu Bamalli ya gaji Sarki Shehu Idris a kasar Zazzau Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Wata hujja da gwamnatin Kaduna ta bada shi ne ba a duba takardun aikin ‘yan takarar ba. Ana ganin cewa an yi wannan ne da nufin cusa Ahmad Bamalli.

An hurowa gwamnatin El-Rufai wuta ta yi la’akari da gidan Mallawa wadanda rabonsu da jin kamshin mulki tun rasuwar Alu Dan Sidi a shekarar 1920.

Ana haka ne sai aka fara rade-radin za a barka masarautar Zazzau. A shekaran jiya gwamna ya gana da majalisar Sarakuna, alamun an fitar da sabon Sarki.

A ranar 7 ga watan Oktoba, aka tabbatar da Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarki. Gwamna ya taya shi murna tare da yi masa fatan alheri a mulki.

Ambasada Ahmed Bamalli shine Sarki na farko daga gidan Mallawa a cikin shekaru 100.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel