Majalisa ta ce gwamnatin Gombe za ta yi wa Masarautun Jiha kwaskwarima

Majalisa ta ce gwamnatin Gombe za ta yi wa Masarautun Jiha kwaskwarima

- Majalisar Jihar Gombe Gwamnati ta na shirin yi wa dokokin masarautu gyara

- Kakakin majalisar Gombe, Rt. Hon. Abubakar Sadiq Ibrahim ya bayyana haka

- Idan aka amince da kudirin, Sarakunan jihar Gombe za su kara martaba da kima

A makon nan ne Gwamnatin jihar Gombe ta aika kudiri zuwa ga majalisar dokokin jihar da nufin ayi wa dokokin masarautu garambawul.

Kakakin majalisar jihar Gombe, Rt. Hon. Abubakar Sadiq Ibrahim, ya tabbatar da cewa fadar gwamna ta aiko masu da wannan kudiri.

Abubakar Sadiq Ibrahim ya ce sabon kudirin zai taimaka wajen yi wa dokokin da su ka kafa masarautun gargajiya ‘yan garambawul.

KU KARANTA: Wanene Sarki Ahmad Bamalli, wanda ya karya tarihin shekaru 100 a Zazzau

Da ya ke magana da manema labarai a ranar 6 ga watan Oktoba, Abubakar Sadiq Ibrahim ya ce dokar za ta gyara sha’anin sarauta a Gombe.

An yi kudirin take da: “A bill to harmonize the provision of all chieftaincy legislations, to repeal and replace those legislations and to make further provisions for Chieftaincy na shekarar 2020.”

Kudirin na 2020 da mai girma gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya gabatar, zai gyara dokokin da su ka ci karo da juna a jihar Gombe.

KU KARANTA: Wani bajimin Malamin da Izala ta ke ji da shi ya rasu a Jihar Yobe

Majalisa ta ce gwamnatin Gombe zai yi wa Masarautun Jiha kwaskwarima
Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya Hoto: The Sun
Asali: UGC

Ya ce: “Gwamna ya na so a gyara dokoki masu-ci saboda sarakunan gargajiya su na bada gudumuwa wajen tafiyar da sha’anin talakawa.”

Shugaban majalisar ya kara da cewa duk da ragewa sarakuna kima da kundin tsarin mulkin 1979 da turawan mallaka su ka yi, ana ganin darajarsu.

Amincewa da wannan kudiri cikin gaggawa zai taimaka wajen karawa masu mulki daraja, tare da shigo da su cikin gwamnati inji Rt. Hon. Ibrahim.

Dazu kun ji cewa ta tabbata Gwamnatin Kaduna ba za ta kawo kudirin raba Masarauta ba. Hon. Sulaiman Dabo ya tabbatar da wannan a Facebook.

Ana haka sai aka ji cewa Ambasada Ahmad Bamalli ya hau kujerar Sarki ya na shekara 54.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel