COVID-19: Trump, Johnson, Albert da ragowar Shugabbanin da su ka yi jinya

COVID-19: Trump, Johnson, Albert da ragowar Shugabbanin da su ka yi jinya

- A shekarar nan annobar cutar COVID-19 ta barke a kasashen Duniya

- Wannan cuta ta kwantar da har manyan shugabannin da ake ji da su

- Donald Trump shi ne na karshe da ya kamu da wannan cuta ta mura

A makon jiya ne aka samu labari cewa cutar COVID-19 ta harbi shugaban kasar Amurka, Donald Trump. Bayan kwanaki kadan a gadon asibiti, ya koma aiki.

#StatiSense ta kawo jerin sauran shugabannin kasashe da dauloli da su ka kamu da wannan cuta ta mura bayan barkewar annobar kafin ta harbi Donald Trump.

1. Donald Trump

A karshen makon da ya wuce, Trump ya kamu da COVID-19, Shugaban Amurkan ya bar asibiti.

2. Boris Johnson

Firayim Ministan Birtaniya, Boris Johnson ya na cikin wanda COVID-19 ta harba. Shugaban ya yi jinya tsakanin Mayu da Afrilu a asibitin St. Thomas a birnin Landan.

3. Michel Barnier

Michel Barnier ya na cikin shugabannin kungiyar Turai ta Duniya watau EU. A watan Maris ya harbu da Coronavirus. Barnier ya na cikin kusoshin BREXIT a EU.

KU KARANTA: An sheka da Donald Trump asibitin sojoji

4. Mikhail Mishustin

Sabon Firayim Ministan kasar Rasha, Mikhail Mishustin ya yi jinyar COVID-19 na wasu ‘yan kwanaki. Daga baya ya samu sauki har ya koma bakin aiki a Mayu.

5. Jair Bolsonaro

Shugaban kasar Brazil ya kamu da ciwon COVID-19 watanni kusan uku da su ka wuce. Bolsonaro ya na cikin shugabannin da su ka yi kunnen kashi wajen rufe fuskarsu.

6. Jeanine Añez

A watan Yuli ne aka yi wa shugaban rikon kwaryar kasar Boliviya gwaji, inda aka tabbatar da cewa ya kamu da COVID-19 tare da wasu Ministocin gwamnatinsa.

KU KARANTA: Turai sun ba Okonjo-Iweala kwarin gwiwar takarar WTO

7. Alexander Lukashenko

Wani shugaban da ya kamu da Coronavirus a shekarar nan shi ne Alexander Lukashenko na kasar Belarus. Har Alexander Lukashenko ya yi ciwo ya gama, bai kwanta ba.

8. Nikol Pashinyan

Firayim Ministan Armeniya, Nikol Pashinyan ya yi fama da COVID-19, ya warke a mako guda.

9. Juan Hernandez

Shugaba Juan Orlando Hernandez ya yi jinyar COVID-19 na makonni a kasar Honduras kwanaki.

10. Prince Albert II

COVID-19 ta kwantar da Yarima Albert na biyu II na Monaco tun daga Maris har farkon Afrilu.

Kun ji cewa an sallami shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump daga asibitin Sojojin Walter Reed da ke Bethesda inda yake jinya bayan kamuwa da cutar Coronavirus.

Shugaban kasan Amurkan ya bayyana hakan da yammacin Litinin a shafinsa na Tuwita.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel