Yan bindiga sun sace tsohon kwamishinan Nasarawa, sun bukaci N30m

Yan bindiga sun sace tsohon kwamishinan Nasarawa, sun bukaci N30m

- Yan bindiga sun sace tsohon kwamishinan ilimi na jihar Nasarawa, Cif Clement Uhembe a gidansa na Lafia

- Masu garkuwan sun kuma bukaci a biya naira miliyan 30 a matsayin kudin fansarsa

- Zuwa yanzu dai ba a ji komai ba daga bakin hukumar yan sanda game da lamarin

Masu garkuwa da mutane a daren ranar Talata, sun sace tsohon kwamishinan ilimi na jihar Nasarawa, Cif Clement Uhembe a gidansa na Lafia.

Yan bindigan sun bukaci a biya naira miliyan 30 a matsayin kudin fansarsa, jaridar The Nation ta ruwaito.

Masu garkuwan, dauke da muggan makamai, sun kai farmaki gidan tsohon kwamishinan wanda ya kuma kasance babban lakcara a sashin kimiyar siyasa a jami’ar tarayya ta Lafia, da misalin karfe 8:30 na dare.

Yan bindiga sun sace tsohon kwamishinan Nasarawa, sun bukaci N30m
Yan bindiga sun sace tsohon kwamishinan Nasarawa, sun bukaci N30m Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

Matar tsohon kwamishinan, Misis Amarya Uhembe, ta fada ma jaridar The Nation cewa masu garkuwan, kimanin su goma, sun kai mamaya gidansu.

Sannan suka fasa daya daga cikin dakunan gidan inda mijinta ke hutawa bayan aiki sannan suka tafi dashi zuwa wani wuri da ba a sani ba.

KU KARANTA KUMA: Garambawul: Dattawan arewa sun mara wa Adeboye baya, sun yi korafi cewa Najeriya ta gaza

A cewarta, “Sun zo da misalin karfe 8:30 na dare sannan suka fara kwankwasa kofa da karfi yayinda mijina ke a uwar-daka. Sai na doshi kofar don ganin wanda ke kwankwasa kofar kawai sai na gano yan bindiga da makamai.

“Lokacin da na lura cewa yan bindiga ne, sai na yi kokarin rufe kofar cikin sauri, ina ta ihun neman agaji kafin mijina ya zo ya same ni a yayinda nake kokarin rufe kofa, yayinda su kuma suke kokarin shigowa falon ta karfin tsiya.

“Mijina ya yi saurin zuwa wajen kofa sannan muka yi nasarar rufe kofar amma yan bindigan suka ci gaba da turawa har said a suka yi nasarar amfani da wasu abubuwa wajen fasa kofar sannan suka shigo.”

Ta bayyana cewa daga baya yan bindigan su bai wa mijin nata wayarsa domin ya kira yan uwansa don kudin fansar naira miliyan 30.

KU KARANTA KUMA: Allahu Akbar: Sakataren masarautar Kano, Muhammadu Bayero ya rasu

Duk kokari na zantawa da hukumomin yan sanda kan lamarin ya ci tura. Kakakin rundunar, Ramhan Nansel bai amsa kiran wayarsa ba.

A wani labarin, yan bindiga sun kai wa mamba mai wakiltan mazabar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai, Rt.Hon. Nicholas Garba Sarkin Noma, hari a ranar Asabar, a hanyar Kwoi-Fadan Kagoma da ke karamar hukumar Jaba a jihar Kaduna.

An tattaro cewa dan majalisar da sauran mutanen da ke motar sun kubuta ba tare da rauni ba, amma dai motarsu ta yi kaca-kaca sakamakon harbe-harben yan bindigan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel