Nwajuiba: Ka yi murabus daga kujerar Minista, ka rungumi noma - Kungiyar ASUU

Nwajuiba: Ka yi murabus daga kujerar Minista, ka rungumi noma - Kungiyar ASUU

- Wani shugaban ASUU ya maidawa Hon. Chukwuemeka Nwajuiba martani

- Ministan ilmin ya bukaci Malaman Jami’a su koma noma idan ba su son aiki

- Farfesa Ayo Akinwole ya ce Ministan ya nuna bai ma san inda aka sa gaba ba

Kungiyar ASUU ta malaman jami’a a Najeriya ta ba karamin ministan ilmi na kasa, Chukwuemeka Nwajuiba, shawarar ya yi murabus daga aikinsa.

Shugaban ASUU na reshen Ibadan, Farfesa Ayo Akinwole ya yi kira ga Hon. Chukwuemeka Nwajuiba da ya bar kujerarsa, ya shiga harkar noma.

Farfesa Ayo Akinwole ya na maida martani ne ga wasu kalamai na Ministan tarayyan inda aka ji ya na caccakan malaman jami’a da ke yajin-aiki.

Malamin makarantar ya ke cewa sukar da Ministan ya fito ya na yi, ya nuna bai san harkar ilmi ba.

KU KARANTA: Sauran Ma'aikatan Jami'a sun bi ASUU, sun tafi yajin - aiki

Ayo Akinwole ya ke cewa kalaman Ministan sun nuna karancin fahimtarsa game da sha’anin ilmi da harkar koyarwa, da yadda gwamnati ta dauki ilmi.

Ya ce: “Idan Ministan ilmi yayi sha’awar noma, sai ya ajiye aikinsa, ya daina nuna rashin saninsa a fili game da matsalolin da ke damun harkar ilmi.”

“Mu na yaki ne domin ganin cewa wadanda ke rike da mukamai sun zama su na sauke nauyin da su ka dauka na yi wa talakawa aiki.” Inji Farfesan.

Akinwole ya fadawa Punch, “Dole su dauki dawainiyar ilimi a makarantun gwamnati. Tun 2009 mu ke fama da albashi guda. Wannan ba zai iya rike mu ba.”

KU KARANTA: Ba da gaske ake son mu janye yajin aiki ba - ASUU

Nwajuiba: Ka yi murabus daga kujerar Minista, ka rungumi noma - Kungiyar ASUU
Chukwuemeka Nwajuiba Hoto: education.gov.ng
Asali: UGC

“Ana tafiyar da jami’o’i ne da gumin malamai, yayin da ‘yan siyasa su ke satar kudin al’umma domin su yi facaka. Ba za mu yarda da IPPIS ba."

Farfesa Akinwole ya ce sun kawo wata manhaja a madadin IPPIS wanda aikinta ya sabawa doka.

A jiya shugaban ASUU ya maidawa Hon. Chukwuemeka Nwajuiba martani. Ministan da ya ce Malamai su koma noma ya ji babu dadi a hannun ASUU.

A jiya kun ji cewa Ministan ya yi kaca-kaca da ASUU, ya ce dole ta tsarin IPPIS za a rika biyan albashi, sai dai idan ba su sha'awar koyarwa, su tafi gona

Ministan ilmi ya ce gwamnati ba ta rike malaman ba, za su iya ajiye aikin na su, su yi gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng