Ganduje ya rantsar da sabbin kwamishinonin KANSEIC uku da sakatarorin dindindin hudu

Ganduje ya rantsar da sabbin kwamishinonin KANSEIC uku da sakatarorin dindindin hudu

- Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa sabbin kwamishinonin hukumar zabe na jihar guda uku

- Sabbin kwamishinonin da aka naɗa sun hada da Muhammad Rufai, Idris Geza da Aishatu Bichi

- Ganduje ya kuma nada sabbin sakatarorin dindindin guda hudu don maye gurbin wasu da suka yi ritaya

Gwamnan Abdullahi Ganduje ya rantsar da sabbin Kwamishinoni uku a hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Kano wato KANSEIC.

Kwamishinonin su ne: Muhammad Rufai, Idris Geza da Aishatu Bichi.

Ganduje ya rantsar da sabbin kwamishinonin KANSEIC uku da sakatarorin dindindin hudu
Ganduje ya rantsar da sabbin kwamishinonin KANSEIC uku da sakatarorin dindindin hudu. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: FG ta bada umurnin sake tantance masu N-Power

A yayin bikin nadin a ranar Talata a Kano, Ganduje ya ce yana kyautata zaton sabbin kwamishinonin za su bada gudunmawarsu wurin ganin anyi zaben kananan hukumomi na 2021 lafiya tare da yiwa kowa adalci.

Ya shawarci sabbin kwamishinonin su kasance masu gaskiya, adalci su kuma hada kai da sauran mambobin hukumar su kuma zama marasa tsoro wurin gudanar da ayyukan su.

Mista Ganduje ya ce: "Ina kira ga sabbin kwamishinonin da aka naɗa su zama masu adalci ga kowa wurin gudanar da ayyukan su.

"Nan gaba za a rantsar da kwamishinonin na hudu duba da cewa har yanzu Majalisar Jihar Kano tana tantance shi."

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe jami'in kwastam da wasu 9 a Katsina

Har wa yau, a ranar Talatan an rantsar da sabbin sakatarorin dindindin hudu da suka hada da Kabiru Magani, Abba Mustapha, Umar Liman da Fatima Sarki.

Gwamnan ya ce an zabe su ne saboda cancantarsu da kuma kwarewar su wurin aiki. An nada su ne don maye gurbin wasu da suka yi ritaya.

Ya ce an nada su ne don ƙarfafa ayyukan gwamnatin jihar.

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan Aliu, masana'antar masu nishadantarwa da gwamnatin jihar Ekiti bisa rashin fitaccen mai wasan drama, Jimoh Aliu.

Jimoh Aliu ya rasu yana da shekaru 80a duniya kamar yadda The Pulse ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel