Ondo 2020: Kasar Amurka ta gargadi Najeriya kan zaben gwamna

Ondo 2020: Kasar Amurka ta gargadi Najeriya kan zaben gwamna

- Kasar Amurka ta bukaci masu ruwa da tsaki da su ci gaba da aikin tabbatar da zabe na gaskiya da lumana a jihar Ondo

- Amurka ta jaddada muradinta na son ganin an bi tsarin dimokradiya, tare da hadin-kan hukumar INEC, jam'iyyun siyasa da jami'an tsaro

- Ta kuma jaddada cewa zata cigaba da mutunta alaka tsakaninta da Najeriya

Kasar Amurka ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a tsarin damokradiyya, ciki harda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), jam’iyyun siyasa, da hukumomin tsaro da su dauki matakan da ya kamata don tabbatar da zabe cikin lumana da muradin mutanen jihar Ondo.

Hukumar zabe ta saka ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, domin gudanar da zaben gwamna a jihar Ondo.

Ofishin jakadancin Amurka a cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba, ta kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su ci gaba da aiki domin tabbatar da zabe na gaskiya da lumana a jihar.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Ƴan bindiga sun kai sabon hari Filato, sun kashe Sarki da mutane huɗu

Ondo 2020: Kasar Amurka ta gargadi Najeriya kan zaben gwamna
Ondo 2020: Kasar Amurka ta gargadi Najeriya kan zaben gwamna Hoto: @USinNigeria
Asali: Twitter

Amurka ta ce zata cigaba da mutunta alaka tsakaninta da Najeriya wajen aiki tare domin cimma muradai da wanzuwar al'umomin kasashen biyu.

Jawabin ya ce: “Kasar Amurka ta bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki da su ci gaba da aiki don zabe mai sahihanci, adalci da kwanciyar hankali a jihar Ondo.

“Muna jadadda burinmu na ganin cewa dukkanin masu ruwa da tsaki a tsarin damokradiyya, ciki harda INEC, jam’iyyun siyasa da hukumomin tsaro sun dauki matakan da ya kamata domin tabbatar da zabe cikin lumana da zai nuna muradin mutanen Ondo.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na ce ba zan yiwa Buhari addu'a ba - Sule Lamido

“Kasar Amurka na nan a kan bakarta na mutunta alaka tsakaninta da Najeriya kamar yadda muke aiki don cimma manufarmu na zaman lafiya da wanzuwar al'umomin kasashen biyu."

A gefe guda, Abdulsalami Abubakar, ya bukaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar da zaman lafiya da zabe na gaskiya a jihar Ondo gabannin zaben gwamna.

Mista Abubakar, wanda ya kasance tsohon shugaban kasa, ya yi kiran ne a cikin wata sanarwa da aka saki a Abuja, a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng