Ondo 2020: Akeredolu ya kara samun karfi yayinda shugaban ZLP da mambobin jam’iyyar suka koma APC
- Jam’iyyar APC a jihar Ondo ta tarbi sabbin mambobi daga jam’iyyar ZLP gabannin zaben gwamna
- Tsohon Shugaban ZLP a karamar hukumar Ondo ta gabas ne ya yi wa masu sauya shekar jagoranci zuwa APC a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba
- Da yake tarban sabbin mambobin, Shugaban APC a jihar Ondo ya ce jam’iyyar ZLP a karamar hukumar Ondo ta gabas ta rushe
Kudirin Gwamna Rotimi Akeredolu na yin tazarce ya samu gagarumin goyon baya a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba, yayinda mambobin jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Akure.
TVC ta ruwaito cewa shugaban ZLP a karamar hukumar Ondo ta gabas, Olamigoke Busayo, wanda ya yi murabus daga jam’iyyar a ranar Lahadi, 4 ga watan Oktoba, ne ya yi wa masu sauya shekar jagora.
KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Ƴan bindiga sun kai sabon hari Filato, sun kashe Sarki da mutane huɗu
Da yake tarban masu sauya shekar, shugaban APC a jihar, Ade Adetimehin, ya ce mafarkin ZLP ya dakushe domin tsarinta ya rushe a yankin Ondo ta gabas.
Ya bayyana tsohon shugaban na ZLP a matsayin sanannen dan siyasa kuma babban kadara ga kowace jam’iyyar siyasa.
Hukumar zabe ta kasa na zaman kanta, ta sanya ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, domin gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo.
KU KARANTA KUMA: Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin mulkin Najeriya - Tanko Yakasai
A gefe guda, gabannin zaben gwamnan Ondo, kimanin jam’iyyun siyasa 11 ne suka hade da jam’iyyar PDP, wanda hakan ya kara wa takarar Eyitayo Jegede (SAN) karfi.
Shugaban jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Oladele Ogunbameru, wanda kuma shine kakakin jam’iyyun siyasan ne ya sanar da hakan a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba, a Akure, babbar birnin jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng