Dalilin da ya sa na ce ba zan yiwa Buhari addu'a ba - Sule Lamido
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce ko shakka babu kasar Najeriya ta samu ci gaba a shekaru 60 da ta yi da samun yancin kai
- Sai dai ya ce nasarorin da kasar ta samu ba su kai yadda ya kamata ba
- Har ila yau jigon na PDP ya yi tsokaci kan salon mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Ya ce duk son sa da Buhari da mutanen gwamnatinsa ba zai shirya ya je masallaci don yi masu zikiri ko salati ba
Babban jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Sule Lamido ya bayyana cewa kasar Najeriya ta cimma wasu nasarori a cikin shekaru sittin, to amma ya ce nasarorin ba su kai yadda ya kamata ba.
Tsohon gwamnan na jihar Jigawa kuma tsohon ministan harkokin wajje ya kuma yi tsokaci kan salon mulkin Shugaban Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.
A wata hira da sashin Hausa na BBC, Lamido ya ce:
“Ba yadda za a yi shekara 60 ace ba a ci gaba ba, dole akwai ci gaba. Amma shin a matsayinmu na kasa manyanmu sun yi amfani da kimiyya wajen gina kasa?
“Girman kasa shi ne kishin shugabanni ga ‘yan kasa wajen ba da gudunmuwa wajen gina su. Saboda haka an ci gaba a Najeriya. Amma ba a yi amfani da abinda Allah ya ba mu ba na ma’adinai na tarihi da arzikin kasa da kimiyya da basira da hikimar shugabanci wajen gina mutane ba."
Da aka tambaye shi kan furucinsa na cewa shugabanni ba su yi amfani da abunda ya kamata ba alhalin shima ya rike mukamin gwamna da minista, Sule ya ce: “Shugabanci ba wai sai kana gwamna ba. Shugabanci kowani fanni akwai shi ai.
KU KARANTA KUMA: Ondo 2020: Abdulsalami ya yi kira ga zaben gwamna na gaskiya da lumana
“Don na yi gwamna shine me? Iyakaci na ga me zan yi a matsayin gwamna, amma ina da sauran ma’aikata ‘yan uwana.
Game da ra’ayinsa kan halin da ake ciki a Najeriya, tsohon gwamnan na Jigawa ya ce: “Ni mai hamayya ne, kuma duk sona da Buhari ko mutanen gwamnatin Buhari ba zan je masallaci in yi salla raka’a biyu in yi musu salati ko zikiri ba, ba zan yi musu ba.
“Tun da shi ne ka ce bai iya ba, shi ne ka gaza, ka wulakanta ka kwace masa mulki, saboda in ya fadi magana za a ce hamayya ce. Saboda haka ba ni da wani matsayi a kan mulkin yanzu. Don haka ina kai aka kore ni.
“Mai wannan hukuncin shine irinka da kuka je kuka yi hayaniya kuna zakin baki, cewa PDP barayi ne, aka zo aka yi yakin neman zabe na rashin hankali na wauta da son zuciya. Aka zo aka jefa kuri’a sai ka je ka tambaye su. Ma’ana wadanda ake wa mulkin su za ka tambaya ba ni ba.
“Saboda haka hukunci yana wajen ‘yan Najeriya ai. Idan lokaci ya yi wajen zabe. Idan ana ganin abinda Buhari yake yi daidai yake yi APC su yi ta mulki har illa masha Allahu. Su yi ta yi. In kuma na ganin mulkin jiki magayi ne, kuma kowa yana ji a jikinsa, toh muna nan a gefe sai a kira mu, mu zo mu gyara kayanmu."
KU KARANTA KUMA: Ku maye gibin kujerun yan majalisar APC jihar Edo - PDP ga INEC
Game da shawarar da zai ba Buhari idan suka gana, Sule ya ce: “Kai, kuna ba ni mamaki wallahi tallahi. Ai babu yadda za a tambaye ni me zan gaya wa Buhari. Tun da muna hamayya mu aka kawar. Ni kishiya ce. Ba zan ba shi shawara ba."
A wani labari na daban, Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ce ya karbi rokon da Aminu Shehu Shagari ya ke yi na neman afuwa game da abin da ya faru a 2015.
Dr. Goodluck Jonathan ya yi magana a shafinsa na Facebook, ya ke cewa shi ya yafe wa Honarabul Aminu Shehu Shagari kamar yadda ya bukata.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://facebook.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng