Ondo 2020: Abdulsalami ya yi kira ga zaben gwamna na gaskiya da lumana

Ondo 2020: Abdulsalami ya yi kira ga zaben gwamna na gaskiya da lumana

- Tsohon shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar ya yi kira ga zabe na gaskiya da lumana a jihar Ondo

- Salami ya ce hakkin jam’iyyun siyasa, masu zabe da kungiyoyin jama’a ne tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yayin gudanar da zaben

- Hukumar INEC ta sanya ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba domin gudanar da zaben gwamnan Ondo

Shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC), Abdulsalami Abubakar, ya bukaci masu ruwa da tsaki da su tabbatar da zaman lafiya da zabe na gaskiya a jihar Ondo gabannin zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba.

Mista Abubakar, wanda ya kasance tsohon shugaban kasa, ya yi kiran ne a cikin wata sanarwa da aka saki a Abuja, a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba.

Ya ce hakkin jam’iyyun siyasa, masu zabe da kungiyoyin jama’a ne tabbatar da zabe na gaskiya da lumana a jihar, jaridar Premium Times ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Ba ni da makiyan fada – Shugaba Goodluck Jonathan ya fadawa Aminu Shagari

“A matsayinmu na masu ruwa da tsaki, mu dauki manufofi na rashin son kai, da kasancewa tsaka-tsaki a yayin zaben,” in ji shi.

Ondo 2020: Abdulsalami ya yi kira ga zaben gwamna na gaskiya da lumana
Ondo 2020: Abdulsalami ya yi kira ga zaben gwamna na gaskiya da lumana Hoto: @THISDAYLIVE
Asali: UGC

Tsohon Shugaban kasar ya bukaci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta zamo a tsakiya sannan ta yi gaskiya a gudanarwar zaben.

“Muna bukatar hukumomin tsaro, INEC, kungiyoyin jama’a, sarakunan gargajiya da masu zabe su goyi bayan zaman lafiya.

“Kwamitin NPC zai ci gaba da wa’azin zaman lafiya a tsarin zaben, abu mai wahala ne canza alkiblar siyasar Najeriya, akwai bukatar duk mu taka rawarmu,” in ji shi.

Abubakar ya kuma bayyana cewa kwamitin zai ci gaba da aiki bisa ka’ida, cewa “mun yi aiki ba ji ba gani domin goyon bayan zaben lumana da mika mulki ba tare da tashin hankali ba.

KU KARANTA KUMA: 2023: Atiku ya magantu a kan fastocin yakin neman zabensa

Ya bayyana cewa koda dai lokacin kafin zabe ya kan zo da tsoron barkewar rikici da barazana ga zaman lafiyar kasa, ya zama dole yan Najeriya su tunkari zabe da zuciya daya.

A gefe guda, gabannin zaben gwamnan Ondo, kimanin jam’iyyun siyasa goma sha daya ne suka hade da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Hakan ya kara wa takarar Eyitayo Jegede (SAN) na PDP karfi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel