Shugaban kasa ya roki Shugabannin Majalisa su yi hakuri da wasu kudirorinsa

Shugaban kasa ya roki Shugabannin Majalisa su yi hakuri da wasu kudirorinsa

- Shugaban kasa ya ce ‘Yan Majalisa su yi hakuri da dokokin da ya ke kai wa gabansu

- Muhammadu Buhari ya yi jawabi a wani taro na musamman da aka shirya a Abuja

- Ana wannan zama ne domin karfafa dankon zumunci tsakanin Buhari da Majalisar

Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan majalisar tarayya su yi hakuri da duk wata doka da ya kawo da su ke da ra’ayin da ta sha ban-bam da shi.

Shugaban Najeriyar ya bukaci majalisa ta yi aiki kan kudirorin da ya kawo kamar yadda al’ada ta ce.

Mai girma Muhammadu Buhari ya yi wannan bayani ne a wajen wani taron hadaka da aka shirya wa ‘yan majalisa da bangaren masu zartarwa.

An shirya wannan zama ne a farkon makon nan a cikin fadar shugaban kasa domin habaka alakar da ke tsakanin bangaroron gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Abin da ya sa duka Jihohi su ka maka Shugaban kasa a kotu

“Bari in yi amfani da wannan dama in tunawa masu kishin kasa; maza da mata cewa sha'anin gwamnati da aikin majalisa abu ne mai canzawa." inji Buhari.

“Ina kiran su zama masu hakuri game da wata doka ko kudiri da za mu kawo da su ke da ta-cewa game da su, su yi aiki kamar yadda aka saba (a doka).”

Shugaban kasar ya tabbatar da cewa burin gwamatinsa shi ne yin abin da zai taimaki kasa baki daya; a samu adalci, zaman lafiya da kuma cigaba.

Buhari ya ke cewa gwamnatinsa ta kawo gyare-gyaren da za su inganta harkar gudanar gwamnati tare da bunkasa karfin tattalin arzikin Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnati ta saki makudan kudi da nufin gano adadin 'Yan Najeriya

Shugaban kasa ya roki Shugabannin Majalisa su yi hakuri da wasu kudirorinsa
Majalisar Tarayya Hoto: Finacial Nigeria
Asali: UGC

A cewarsa hanzarin amincewa da kasafin kudin 2020, da karbar sunayen wadanda za a ba mukamai da majalisa ta yi, ya nuna hadin-kan da ake samu.

Jaridar This Day ta na ganin cewa shugaban kasar ya yi wannan magana ne bayan ‘yan majalisar wakilai sun yi masa fatali da kudirin kudin ruwa.

Kwanakin baya mun kawo maku jerin wasu 'yan majalisar wakilai da su ka fi kawo kudirorin samar da ci gaba a kasa a majalisar wakilan tarayya.

Daga ciki akwai Nkeiruka Onyejeocha, Nkem Abonta, Nicholas Ossai, da Dachung Bagos. Akwai kuma irinsu Gideon Gwani, da kuma Hon. Francis Uduyok.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng