Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi wa Jam’iyyar PDP da Eyitayo Jegede kamfe a Ore

Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi wa Jam’iyyar PDP da Eyitayo Jegede kamfe a Ore

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya je jihar Ondo, ya na yi wa PDP kamfe

- Babban ‘Dan siyasar ya yi kira ga mutanen Arewa da ke Ore su zabi PDP

- Za a yi zaben Gwamnan Jihar Ondo a Ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba

Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga jihar Ondo inda ya fara taya jam’iyyar PDP mai hamayya yakin neman zaben gwamna.

Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da dinbin magoya bayan jam’iyyar PDP da kuma masoya darikarsa ta Kwankwasiyya da ke jihar Ondo.

Kamar yadda tsohon gwamnan na Kano ya bayyana, an yi wannan taro ne a garin Ore, jihar Ondo.

Sanata Kwankwaso ya hadu da mutanen Arewacin Najeriya da ke zama a yankin Ore ne tare da ‘dan takarar mataimakin gwamna na PDP.

KU KARANTA: Obaseki: Kwankwaso ya jawo ra'ayin Hausawa a Edo

Mista Ikengboju Gboluwaga shi ne ya yi wa Rabiu Kwankwaso da sakataren kudi na PDP, Malam Abdullahi Mai Basira iso wajen mutanen jihar.

Kwankwaso ya tabbatar da wannan haduwa jiya, ya ce: “Mu na Ore a yau da rana, kuma taro ya yi taro.

“Mun gode garin Ore da ku ka marawa ‘dan takararmu, Eyitayi Jegede SAN na jam’iyyar PDP da abokin takararsa, Ikengboju Gboluwa baya.”

Tsohon Ministan na tarayya ya yi kira ga dinbin mutanen da su ka fito wajen wannan gangami su tabbatar sun zabi PDP a ranar 10 ga watan nan.

KU KARANTA: Kwankwaso da manyan 'Yan siyasa sun halarci auren Atiku da Ribadu

Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi wa Jam’iyyar PDP da Eyitayo Jegede kamfe a Ore
Kwankwasiyya a Ondo Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Asali: Twitter

Bidiyon da Rabiu Kwankwaso ya wallafa ya nuna tarin mutane su na cashewa da wasannin Tijjani Gwandu, mawakin da aka dauko daga Kano.

Tijjani Gwandu ya yi wa Eyitayi Jegede waka, ya na kiran mutanen Ondo su ba shi kuri’a.

Wadanda su ka yi wa Kwankwasiyya rakiya sun hada da jagororin tafiyar; Abba Gida-Gida, da ‘yan wasa Sanusi Oscar wanda aka fi sani da Oscar 442.

Idan za ku tuna, watan jiya, PDP ta tura tsohon Gwamnan na Kano zuwa Jihar Edo a lokacin da ake shirin zabe Godwin Obaseki da Osagie Ize-Iyamu.

A dalilin haka ne kuma PDP ta samu goyon bayan wasu Mutanen Arewa da Mahauta a Edo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel