Bode George: Shugabannin PDP na Jihar Legas sun ce Fayose ya nemi afuwa
- Jam’iyyar PDP ta yi tir da wasu kalamai da Ayo Fayose ya yi a jihar Legas
- Tsohon Gwamnan ya fito ya na kiran ayi wa Bode George ritaya a siyasance
- Wadannan kalamai sun fusata PDP, an bukaci ‘dan siyasar ya nemi afuwa
Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Legas ta ba tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, mako guda ya janye maganganun da ya yi, ya na sukar manyan jam’iyya.
PDP ta bukaci Ayodele Peter Fayose ya nemi afuwa na kalaman da ya yi da gan-gan, na babu gaira babu dalili ya na caccakar shugabannin jam’iyya na Legas.
Mai magana da yawun bakin babbar jam’iyyar hamayyar a Legas, Taofik Gani, ya fitar da jawabi ya na zargin Ayodele Peter Fayose da harzuka matasa.
KU KARANTA: Buhari ya bayyana wadanda su ke kawo cikas wajen yin zaben gaskiya
Taofik Gani ya ke cewa a wajen kamfe, tsohon gwamnan ya yi kokarin zuga matasa su yi wa wasu shugabannin jam’iyyarsu ta PDP na jihar Legas bore.
Ayo Fayose ya yi magana kwanaki ta bakin hadiminsa, Lere Olayinka, ya na cewa dole jam’iyyar PDP ta yi wa Cif Bode George ritaya daga siyasa a Legas.
Fayose ya bayyana wannan ne wajen taya PDP yakin neman zaben kujerar Sanatan gabashin Legas.
Kakakin PDP a jihar Kudu maso yammacin kasar ya yi kira ga tsohon gwamnan na Ekiti da ya guji zama mummunan tasiri ga matasan jam’iyya masu tasowa.
KU KARANTA: Yadda rikici ya barkewa PDP a wasu Jihohin Najeriya
“Mugun mutumi, mai kokarin kawo cikas, sabon shiga siyasa ne kurum zai rika kokarin tada rikici, ya na jawo makiya, yayin da ake shirin babban zabe.”
“Mu na shirin muhimmin zabe a jihar nan wanda zai kai mu ga karbe Legas a babban zaben 2023.” Gani ya tunawa Fayose wanda ya bar mulki a 2018.
PDP ta ba ‘dan siyasar zuwa 12 ga Oktoba ya bada hakuri, idan ba haka ba, ta ce za ta rike Fayose da laifi idan aka rasa zabe a Legas da yankin Kudu maso yamma.
Tun a bara ku ka ji cewa ana rigima tsakanin Sanatar Ekiti, Sanata Biodun Olujimi da Ayo Fayose a kan takarar shugaban kasar Atiku Abubakar a jam'iyyar PDP.
Bayan nan kuma kwanaki Ayo Fayose ya yi kokarin hana wani kigon APC dawowa PDP a Ekiti.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng