Zaben Gwamna: Kotu ta ba Diri da Jam’iyyar PDP gaskiya a Jihar Bayelsa

Zaben Gwamna: Kotu ta ba Diri da Jam’iyyar PDP gaskiya a Jihar Bayelsa

- Kotu ta yanke hukunci a korafin shari’ar zaben Gwamnan Jihar Bayelsa

- Alkalan kotun daukaka kara sun bayyana cewa lallai PDP ta ci zabe sarai

- Kafin yanzu kotun sauraron kukan zabe ta rusa nasarar da PDP ta samu

A ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba, 2020, babban kotun daukaka ta yanke hukunci game da shari’ar zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto dazu cewa Alkalan babban kotun tarayya sun ruguza shari’ar da aka yi a ranar 17 ga watan Agustan 2020.

Alkalai biyar su ka saurari shari’ar a karkashin Adezila Mshelia, inda su ka rushe hukucin da kotun sauraron korafin zabe ta zartar kwanaki.

KU KARANTA: Gwamnan Legas ya yi wa APC kamfe a Ondo

Idan za ku tuna kotun da ke sauraron kukan zaben Bayelsa ta soke nasarar Duoye Diri, ta kuma umarci a shirya sabon zaben gwamna a jihar.

Douye Diri da jam’iyyarsa ta PDP sun daukaka kara zuwa kotun gaba, a sakamakon haka kuma sun samu nasara a hukuncin da aka zartar yau.

Alkalan kotun daukaka karan da ke zama a babban birnin tarayya Abuja, sun gamsu cewa PDP ce ta lashe zaben da aka yi a Nuwamban 2019.

Bayan Sanata Douye Diri, hukumar zabe ta kasa watau INEC ta daukaka kara zuwa gaba, ta na kalubalantar hukuncin da kotu ta yi a Agusta.

KU KARANTA: Deltawa sun ji dadin jirgin da Buhari ya kawo mana – Gwamna Okowa

Zaben Gwamna: Kotu ta ba Diri da Jam’iyyar PDP gaskiya a Jihar Bayelsa
Gwamna Douye Diri Hoto: Legit
Asali: UGC

Alkalan babban kotun sun zartar da cewa ba a cire jam’iyyar ANDP daga cikin masu takara a zaben gwamnan Bayelsa ba tare da hakki ba.

Har zuwa yanzu, Legit.ng ba ta samu cikakken rahoto game da wannan hukunci da aka yi ba.

Kotu ta yanke hukunci a korafin shari’ar zaben Gwamnan Bayelsa, an ba PDP gaskiya. Kafin yanzu kotun sauraron kukan zabe ta rusa nasarar PDP.

Kwanaki kun samu rahoton sabani da aka samu tsakanin jihar Ribas da gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, game da rijiyoyin man da ke yankin Soku.

Nyesom Wike ya maidawa Diri martani na cewa a daina biyan Ribas kason kudin man yankin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel